Najeriya za tayi sabbin jiragen yaki 20 a shekarar nan, Hukumar NAF

Najeriya za tayi sabbin jiragen yaki 20 a shekarar nan, Hukumar NAF

- Gwamnatin Najeriya tay odan jiragen yaki don yiwa yan ta'adda ruwan wuta

- Akalla ashirin cikin wadannan jirage zasu iso Najeriya wannan shekarar, cewar NAF

- Yan majalisa kwanakin baya sun ziyarci Amurka don ganin wadannan jirage

Hukumar mayakan saman Najeriya NAF za tayi sabbin jiragen yaki iri-iri guda ashirin kafin karshen shekarar nan, Babban hafsan hukumar, Air Marshal Oladayo Amao, ya bayyana.

Babban hafsan ya bayyana hakan ne a bikin yaye sabbin Sojojin Sama 1,031 a sansanin NAF dake jihar Kaduna, rahoton TheNation.

Sabbin mayakan sun yi karatu da horo ne a makarantar horon Sojin sama.

Amao ya bayyana cewa jiragen yakin Super Tucano takwas zasu zo daga Amurka da Sin a watan Yuli.

A cewarsa, "Hukumar NAF na sa ran samun jirage takwas a Yulin 2021; jirgin A-29 Super Tucano guda 6 daga Amurka, da kuma UCAV guda biyu daga wajen Sin."

"Sauran A-29 Super Tucano guda shida zasu iso a watan Satumba, yayinda CH-3 guda biyu da CH-4 UCAV guda 4 zasu iso kafin karshen shekara."

KU KARANTA: Amurka tayi Alla-wadai da haramta Tuwita a Najeriya da Buhari yayi

Najeriya za tayi sabbin jiragen yaki 20 a shekarar nan, Hukumar NAF
Najeriya za tayi sabbin jiragen yaki 20 a shekarar nan, Hukumar NAF
Asali: Depositphotos

KU DUBA: Amurka tayi Alla-wadai da haramta Tuwita a Najeriya da Buhari yayi

A bangare guda, hukumar yan sanda a jihar Kebbi a ranar Asabar ta tabbatar da kisan mutum 88 da tsagerun yan bindiga suka yi a karamar hukumar Danko/Wasugu na jihar Kebbi.

Kakakin hukumar, Nafi'u Abubakar ya bayyana cewa wannan ya auku ne duk a ranar Alhamis, rahoton NAN.

Yace an kasheshu ne a hare-haren da aka kai garuruwa takwas a karamar hukumar.

A cewarsa, kawo yanzu an gani gawawwakin mutum 88 kuma an tura jami'ai tabbatar da tsaro a yankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel