Da Ɗuminsa: Aisha Buhari Ta Dakatar Da Amfani Da Shafinta Na Twitter

Da Ɗuminsa: Aisha Buhari Ta Dakatar Da Amfani Da Shafinta Na Twitter

- Aisha Buhari, mai dakin shugaban kasar Nigeria, Muhammadu Buhari ta dakatar da amfani da shafinta na Twitter

- Hakan na zuwa ne bayan da gwamnatin Nigeria ta dakatar da ayyukan shafin na Twitter a kasar a ranar Juma'a

- Gwamnatin Nigeria ta dakatar da Twitter ne kan zargin ana amfani da shafin wurin raba kawunan yan kasa ta tada zaune tsaye

Mai dakin Shugaba Muhammadu Buhari, First Lady, Aisha Buhari ta dakatar da amfani da shafinta na Twitter bayan da gwamnatin Nigeria ta dakatar da shafin daga gudanar da ayyukansa a Nigeria.

A wani mataki da ya yi kama da nuna goyon baya ga gwamnatin Nigeria, mai dakin shugaban kasar ta wallafa sako a daren jiya Juma'a 4 ga watan Yuni tana mai cewa za ta dakatar da shafinta na Twitter.

Da Ɗuminsa: Aisha Buhari Ta Dakatar Da Amfani Da Shafinta Na Twitter
Da Ɗuminsa: Aisha Buhari Ta Dakatar Da Amfani Da Shafinta Na Twitter. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Da Duminsa: Aisha Ta Yi Wa Buhari Kara, Ta Dakatar Da Shafinta Na Twitter
Da Duminsa: Aisha Ta Yi Wa Buhari Kara, Ta Dakatar Da Shafinta Na Twitter. Hoto: @aishambuhari
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Da Ɗuminsa: 'Yan Bindiga Sun Sace Wani Ɗan Kasuwa a Kano

Ministan sadarwa da al'adu, Lai Mohammed ne ya sanar da dakatarwa a ranar Juma'a a Abuja, yana mai cewa ana amfani da shafin wurin aikata abubuwa da ke barazana ga hadin kan Nigeria.

Ministan ya kuma ce gwamnatin tarayya ta umurci Hukumar Kula da Kafafen Watsa Labarai, NBC, ta fara aikin bada lasisi ga dukkan dandalin sada zumunta ake amfani da su a kasar.

"Zan dakatar da amfani da shafin Twitter na a yanzu. Allah ya ja zamanin Jamhuriyar Tarayyar Nigeria," kamar yadda ta rubuta.

Aisha Buhari, wacce ta fara amfani da shafin Twitter a shekarar 2016, tana da masu bibiyar shafinta fiye da miliyan daya.

KU KARANTA: Bayan Karɓar N10m, Ƴan Bindiga Da Suka Sace ‘Nurses’ a Kaduna Sun Ce a Ƙaro Musu N30m

First Lady din ta kasance mai amfani da shafinta na Twitter wurin wallafa ayyukan da ta ke yi, a wasu lokutan ma ta kan soki wasu daga cikin tsare-tsaren gwamnati.

A wani rahoton daban kun ji cewa Ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani, Dr. Isa Pantami ya yi ikirarin cewa tsarin da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ya bullo da shi na tursasawa yan Nigeria mallakar lambar yan kasa wato NIN, ya rage garkuwa da mutane da harin yan bindiga, The Punch ta ruwaito.

Tribune ta ruwaito cewa Pantami ya yi wannan ikirarin ne a Abuja, a ranar Alhamis, yayin da ya ke bada ba'asi kan nasarorin da ya samu tun fara aiki a shekarar 2019.

Asali: Legit.ng

Online view pixel