Bayan Karɓar N10m, Ƴan Bindiga Da Suka Sace ‘Nurses’ a Kaduna Sun Ce a Ƙaro Musu N30m

Bayan Karɓar N10m, Ƴan Bindiga Da Suka Sace ‘Nurses’ a Kaduna Sun Ce a Ƙaro Musu N30m

- Yan bindiga da suka sace malaman jinya a Kaduna sun nemi a biya N30m kafin su sako su

- Hakan na zuwa ne bayan an riga an biya yan bindigan N10m da kuma N450,000

- A halin yanzu yan bindigan sun ce ba za su sake magana da kowa ba sai an biya su karin N30m

Yan bindigan da suka sace ma'aikan jinya biyu a babban asibitin Doka, karamar hukumar Kajuru na jihar Kaduna sun nemi a biya su Naira miliyan 30 kafin su sako su, The Nation ta ruwaito.

Shugaban kungiyar Malaman jinya da unguwan zoma, NANNM, reshen jihar Kaduna, Kwamared Ishaku Yakubu, ya shaidawa manema labarai ya shaidawa manema labarai cewa masu garkuwar sun karbi Naira miliyan 10 daga hannun iyalan malaman jinyar.

Bayan Karɓar N10m, Yan Bindiga da Suka Sace ‘Nurses’ a Kaduna Sun Ce a Ƙaro Musu N30m
Bayan Karɓar N10m, Yan Bindiga da Suka Sace ‘Nurses’ a Kaduna Sun Ce a Ƙaro Musu N30m. Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Hotunan Muggan Makaman Da Ƴan Sanda Suka Ƙwato Daga Hannun Masu Garkuwa Da Ƴan Bindiga

A cewarsa, "Da farko masu garkuwar sun nemi Naira miliyan 10, katin waya na N50,000 da wayoyin salula kirar Tecno hudu wanda aka kai musu makonni biyu da suka wuce. Bayan karbar N10m, sun nemi a kara musu kudi.

"Mutanen gari ne suka yi karo-karo aka tara N10m din na farko da aka bai wa yan bindigan.

"Sau biyu aka biya su kudi kafin a biya N10m din na farko, da farko sun karbi N2.5m, bayan makonni biyu aka sake kai musu N7.5m amma duk da hakan ba su saki malaman jinyar ba don suna son a karo musu N30m, abin ba dadi.

KU KARANTA: Da Ɗuminsa: Mai Yiwuwa In Fito Takarar Shugaban Ƙasa a 2023, Yahaya Bello

"Yan bindigan sun karbi N450,000 daga yan uwan wadanda suka yi garkuwa da su baya ga N10m din. Yan bindigan sun ce ba za su yi magana da kowa ba sai an biya kudin da suka sake nema."

A wani labarin daban, daliban makarantun sakandare a jihar Kano sun yi kira ga gwamnatin jihar ta samarwa dalibai mata audugan mata kamar yadda ta ke samar da littafan karatu kyauta, Vanguard ta ruwaito.

Daliban sun koka da cewa yan mata da yawa ba su da kudin siyan audugan matan, don haka suke rokon gwamnatin ta taimaka musu domin su samu su rika tsaftace kansu.

Sun yi wannan rokon ne yayin wani taron wayar da kai na kwana daya da aka yi kan tsaftar mata da jiki da Kungiyar Yan Jarida Masu Rahoto Kan Bangaren Lafiyar Mata reshen jihar Kano suka shirya don bikin ranar Al'adar Mata Ta Duniya na 2021'

Asali: Legit.ng

Online view pixel