Masu Garkuwa Da Ƴan Bindiga Sun Ragu Saboda NIN, In Ji Pantami

Masu Garkuwa Da Ƴan Bindiga Sun Ragu Saboda NIN, In Ji Pantami

- Dr Isa Pantami, ministan sadarwar da tattalin arzikin zamani, ya ce bullo da NIN ya rage garkuwa da mutane da harin yan bindiga

- Pantami ya yi wannan ikirarin ne a ranar Alhamis a Abuja yayin da ya ke bayanin nasarorin da ma'aikatarsa ta samu tun fara aikinsa a 2019

- Mataimakin shugaban NCC, Farfesa Umar Danbatta ya ce a yanzu masu garkuwa sun koma amfani da wayoyin wadanda suka yi garkuwa da su

Ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani, Dr. Isa Pantami ya yi ikirarin cewa tsarin da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ya bullo da shi na tursasawa yan Nigeria mallakar lambar yan kasa wato NIN, ya rage garkuwa da mutane da harin yan bindiga, The Punch ta ruwaito.

Tribune ta ruwaito cewa Pantami ya yi wannan ikirarin ne a Abuja, a ranar Alhamis, yayin da ya ke bada ba'asi kan nasarorin da ya samu tun fara aiki a shekarar 2019.

Masu Garkuwa Da Ƴan Bindiga Sun Ragu Saboda NIN, In Ji Pantami
Masu Garkuwa Da Ƴan Bindiga Sun Ragu Saboda NIN, In Ji Pantami. Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Karin Bayani: Sojan Da Ya Bindige Jami'an Kwastam Har Lahira a Legas Ya Kashe Kansa

Ya ce, "Lokacin da aka nada ni in jagoranci sashin a ranar 24 ga watan Agustan 2019, ana amfani da katin waya wadanda ba a yi rajista ba ko wadanda ba a kammala rajistan ba wurin aikata laifuka. Babu wanda ya san adadin layukan waya marasa rajista.

"Cikin kwanaki 15 da kama aiki, mun tuntubi NCC a matsayinsu an masu kula da harkar. Mun umurci suyi bincike su gano adadin layin waya marasa rajista. Sun gano miliyan 9.4 wanda ya kai adadin mutanen wasu kasashen. Wannan ne karo na farko da muka san adadin layukan waya marasa rajista a kasar nan.

Pantami ya ce daga nan ya umurci NCC ta tabbatar da cewa layukan wayoyi masu rajista na kwarai ne kawai za su rika aiki a kasar kuma an cimma hakan zuwa Satumban 2021.

KU KARANTA: Musulmi Na Da Kotun Musulunci, Muma a Bamu Kotun Kirista, Ƙungiyar CAN Ta JIhar Bauchi

"Daga Satumban 2019 zuwa 2020, za ka lura cewa an samu saukin garkuwa da mutane da harin yan bindiga. A baya da wuya a yi wata daya ko fiye ba tare da ka ji labarin garkuwa da mutane ba.

"A yayin da ka ke kokarin dakile hanyoyin da miyagu ke amfani da su wurin aikata laifi, miyagun za su rika bullo da sabbin hanyoyi."

Mataimakin shugaban NCC, Farfesa Umar Danbatta ya ce a yanzu masu garkuwa na amfani da wayoyin wadanda suka sace ne domin karbar kudin fansa amma ya ce gwamnati na aiki don ganin yadda za ta magance lamarin.

A wani labarin daban, Hukumar Yaki Da Hana Safarar Miyagun Kwayoyi na Kasa, NDLEA, ta ce ta kama wasu mutane da ake zargi da safararmiyagun kwayoyi a birnin tarayya Abuja, The Cable ta ruwaito.

Femi Babafemi, kakakin NDLEA, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi ya ce an kama su ne sakamakon samamen da hukumar ta yi cikin wannan makon.

Cikin wanda aka kama akwai wata Ese Patrick da ake zargi na siyar da miyagun kwayoyi a dandalin Instagram.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164