Da Ɗuminsa: 'Yan Bindiga Sun Sace Wani Ɗan Kasuwa a Kano

Da Ɗuminsa: 'Yan Bindiga Sun Sace Wani Ɗan Kasuwa a Kano

- Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sace wani dan kasuwa a Kano

- Rahotanni sun bayyana cewa yan bindigan sun kutsa garin Kore ne a ranar Alhamis suka sace shi

- Rundunar yan sandan jihar Kano ta tabbatar da sace dan kasuwar tana mai cewa ta tura jami'ai su ceto shi

Yan bindiga sun kutsa garin Kore a karamar hukumar Danbatta na jihar Kano, a ranar Alhamis, suka sace wani dan kasuwa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Rundunar yan sandan jihar Kano ta tabbatar da sace dan kasuwar da wasu yan bindigan da ba a san ko su wanene ba suka yi.

Da Ɗuminsa: 'Yan Bindiga Sun Sace Wani Ɗan Kasuwa a Kano
Da Ɗuminsa: 'Yan Bindiga Sun Sace Wani Ɗan Kasuwa a Kano. Hoto: @Vangaurdngrnews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Hotunan Muggan Makaman Da Ƴan Sanda Suka Ƙwato Daga Hannun Masu Garkuwa Da Ƴan Bindiga

The Nation ta ruwaito cewa yan bindiga, masu yawa sun kutsa garin suna ta harbe-harbe kafin suka yi awon gaba da dan kasuwar mai suna Emmanuel Eze.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce kwamishinan yan sandan jihar, Sama'ila Shua'ibu Dikko, ya riga ya tura jami'an yan sanda domin su tabbatar sun ceto wanda aka sace din cikin koshin lafiya.

A halin yanzu masu garkuwar ba su riga sun tuntubi iyalansa ba domin neman kudin fansa, amma afkuwar lamarin ya jefa mutanen unguwar cikin firgici.

KU KARANTA: Masu Garkuwa Da Ƴan Bindiga Sun Ragu Saboda NIN, In Ji Pantami

Wannan na zuwa ne kwana guda bayan Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya ankarar da rundunar sojojin Nigeria cewa yan bindiga sun fara taruwa a dazukan jiharsa.

A wani labarin daban, daliban makarantun sakandare a jihar Kano sun yi kira ga gwamnatin jihar ta samarwa dalibai mata audugan mata kamar yadda ta ke samar da littafan karatu kyauta, Vanguard ta ruwaito.

Daliban sun koka da cewa yan mata da yawa ba su da kudin siyan audugan matan, don haka suke rokon gwamnatin ta taimaka musu domin su samu su rika tsaftace kansu.

Sun yi wannan rokon ne yayin wani taron wayar da kai na kwana daya da aka yi kan tsaftar mata da jiki da Kungiyar Yan Jarida Masu Rahoto Kan Bangaren Lafiyar Mata reshen jihar Kano suka shirya don bikin ranar Al'adar Mata Ta Duniya na 2021'

Asali: Legit.ng

Online view pixel