Cocin Kotolika Da Haramtawa Mbaka Tsoma Baki a Batutuwan Siyasa

Cocin Kotolika Da Haramtawa Mbaka Tsoma Baki a Batutuwan Siyasa

- Cocin Kotolika a Enugu ya haramtawa Rabaran Fada Ejike Mbaka tsokaci kan batutuwan siyasa

- Wannan umurnin na kunshe ne cikin wasikar da cocin ta aike wa Mbaka a yayin da ya ke daf da dawowa aiki

- Kimanin wata daya da ya gabata, cocin ya dakatar da Mbaka biyo bayan rikicinsa da fadar shugaban kasa kan neman Buhari ya yi murabus

Cocin darikar katolika ta haramtawa Rabaran Fada Ejike Mbaka, shugaban Adoration Ministeries Enugu Nigeria, (AMEN) yin tsokaci kan batutuwan siyasa, The Cable ta ruwaito.

A cikin wasikar da ta aike wa Mbaka kamar yadda wakilin majiyar Legit.ng ya gani, Callistus Onaga, Bishop din Enugu ya kuma mayar da Adoration Ministry wani reshe na cocin kotolika.

Kocin Kotolika Da Haramtawa Mbaka Tsoma Baki Kan Harkokin Siyasa
Kocin Kotolika Da Haramtawa Mbaka Tsoma Baki Kan Harkokin Siyasa. Hoto: @thecableng
Asali: Instagram

DUBA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Gwamnati Ta Dakatar Da Shafin Twitter a Nigeria

Hakan na nufin cewa ba kamar yadda a baya Mbaka ke kula da harkoki a Adoration Ministry ba, a yanzu Bishop din na Enugu zai zabi fasto da zai rika jagorantar ayyuka a can.

Duk da cewa Bishop din ya ce Mbaka zai cigaba da jagoranci a cocinsa, ya kara da cewa yana da ikon nada wani da zai rika tallafa masa wurin ayyukan cocin, Sahara Reporters ta ruwaito.

Wasikar, mai dauke da kwanan wata na ranar 3 ga watan Yuni tana dauke da dokoki da ka'idoji da ake son limaman cocin katolika su rika bi a koda yaushe.

An bada wannan dokokin ne a yayin da Mbaka ke daf da dawowa aiki a cocin bayan dakatar da shi da aka yi na wata guda.

KU KARANTA: Matawalle Ya Sauke Dukkan Ciyamomi Da Kansiloli a Jihar Zamfara

An dakatar da shi ne biyo bayan cece-kuce da suka auku sakamakon musayar maganganu tsakaninsa da fadar shugaban kasa inda ya rika kira da Shugaba Buhari ya yi murabus.

Ya zargi gwamnati da kasancewa a bayan kashe-kashe da dama a fadin kasar tare da yi wa kungiyoyin yan aware kallon yan ta'adda maimakon mayar hankali kan sama musu ayyukan yi.

Malamin ya kuma nuna fushinsa ga ayyukan makiyaya da ke lalata gonakin mutane ba tare da wata damuwa ba.

A wani labarin daban, daliban makarantun sakandare a jihar Kano sun yi kira ga gwamnatin jihar ta samarwa dalibai mata audugan mata kamar yadda ta ke samar da littafan karatu kyauta, Vanguard ta ruwaito.

Daliban sun koka da cewa yan mata da yawa ba su da kudin siyan audugan matan, don haka suke rokon gwamnatin ta taimaka musu domin su samu su rika tsaftace kansu.

Sun yi wannan rokon ne yayin wani taron wayar da kai na kwana daya da aka yi kan tsaftar mata da jiki da Kungiyar Yan Jarida Masu Rahoto Kan Bangaren Lafiyar Mata reshen jihar Kano suka shirya don bikin ranar Al'adar Mata Ta Duniya na 2021'

Asali: Legit.ng

Online view pixel