'Daliban Kano Sun Roki Ganduje Ya Riƙa Basu Audugan Mata Kyauta

'Daliban Kano Sun Roki Ganduje Ya Riƙa Basu Audugan Mata Kyauta

- Daliban makarantun sakandare a jihar Kano sun roki gwamnati ta rika basu audugan mata kyauta kamar yadda ta ke basu littafan karatu

- Daliban sun yi wannan kiran ne a yayin wani taron wayar da kai na kwana daya da aka yi a Kano don bikin ranar Tsaftar Al'adar Mata na duniya

- A yayin taron, kwararru a bangare lafiya sun bawa daliban shawarwari game da tsafta musamman yayin al'ada sannan an rabawa daliban audugan mata

Daliban makarantun sakandare a jihar Kano sun yi kira ga gwamnatin jihar ta samarwa dalibai mata audugan mata kamar yadda ta ke samar da littafan karatu kyauta, Vanguard ta ruwaito.

Daliban sun koka da cewa yan mata da yawa ba su da kudin siyan audugan matan, don haka suke rokon gwamnatin ta taimaka musu domin su samu su rika tsaftace kansu.

'Daliban Kano Sun Roki Ganduje Ya Riƙa Basu Audugan Mata Kyauta
'Daliban Kano Sun Roki Ganduje Ya Riƙa Basu Audugan Mata Kyauta. Hoto: @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Hotunan Muggan Makaman Da Ƴan Sanda Suka Ƙwato Daga Hannun Masu Garkuwa Da Ƴan Bindiga

Sun yi wanna rokon ne yayin wani taron wayar da kai na kwana daya da aka yi kan tsaftar mata da jiki da Kungiyar Yan Jarida Masu Rahoto Kan Bangaren Lafiyar Mata reshen jihar Kano suka shirya don bikin ranar Al'adar Mata Ta Duniya na 2021.

A yayin jawabinta, kwararriya a bangaren lafiya, Matron Rabi Hassan da ke aiki a wani asibiti mai zaman kansa ta bukaci daliban su rika tsaftace jikinsu da muhallinsu don gujewa kamuwa da cututtuka masu yaduwa.

"Ku rika takatsantsan a lokacin al'adar ku, ku rika canja audugar al'ada sau biyu ko uku a kowanne rana bisa la'akari da yadda naku al'adar ta ke"

"Muna baku shawarar cewa ku rika neman shawarar kwararru masana lafiya a duk lokacin da kuka lura wani abu ya sauya game da al'adan ku sannan ku kasance masu tsafta," in ji Hassan.

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Kashe AIG Christopher Dega a Jos

Tunda farko, shugaban makarantar na gwamnati, Suwaiba Isah ta yi kira ga sauran kungiyoyi da mutane masu hali su yi koyi da irin wannan karamcin da kungiyar ta yi.

A yayin taron, kungiyar yan jaridar tare da tallafin gidauniyar Adamu Abubakar Gwarzo sun raba wa daliban audugan mata kyauta.

A wani labarin daban, Hukumar Yaki Da Hana Safarar Miyagun Kwayoyi na Kasa, NDLEA, ta ce ta kama wasu mutane da ake zargi da safararmiyagun kwayoyi a birnin tarayya Abuja, The Cable ta ruwaito.

Femi Babafemi, kakakin NDLEA, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi ya ce an kama su ne sakamakon samamen da hukumar ta yi cikin wannan makon.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel