Matawalle Ya Sauke Dukkan Ciyamomi Da Kansiloli a Jihar Zamfara

Matawalle Ya Sauke Dukkan Ciyamomi Da Kansiloli a Jihar Zamfara

- Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya sauke shugabannin kananan hukumomi a jiharsa

- Matawalle ya dauki wannan matakin ne biyo bayan karewar karin wa'adin watanni shida da aka yi musu a baya

- Gwamnan ya yi musu godiya matuka bisa ayyukan da suka yi wa jihar ta Zamfara kana ya yi musu fatan alheri

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya amince da sauke dukkan shugabannin riko na kananan hukumomin a jiharsa daga ranar Juma'a 4 ga watan Yunin shekarar 2021, The Nation ta ruwaito.

Hakan na zuwa ne bayan karewar karin wa'adin da aka yi musu na watanni shida wadda majalisar dokokin jihar Zamfara ta amince da shi a baya amma yazo karshe a ranar Juma'a.

DUBA WANNAN: Hotunan Muggan Makaman Da Ƴan Sanda Suka Ƙwato Daga Hannun Masu Garkuwa Da Ƴan Bindiga

Matawalle Ya Suke Dukkan Ciyamomi Da Kansiloli a Jihar Zamfara
Matawalle Ya Suke Dukkan Ciyamomi Da Kansiloli a Jihar Zamfara. Hoto: @TheNationNews
Asali: Facebook

Ya bukaci shugabannin na kananan hukumomin su mika mulki ga manyan direktoci a hukumominsu ba tare da bata lokaci ba.

KU KARANTA: 'Karin Bayani: Sojan Da Ya Bindige Jami'an Kwastam Har Lahira a Legas Ya Kashe Kansa

Gwamnan ya yi musu godiya bisa hidimar da suka yi wa jihar sannan ya yi musu fatan alheri a duk wani abin da za su yi a gaba.

Idan za a iya tunawa a baya-bayan nan gwamnan na Zamfara ya sauke kwamishinoni da shugabannin hukumomi da ma'aikatu a jiharsa.

Cikin wadanda abin ya shafa har da sakataren gwamnatin jiha, shugaban ma'aikatan fadar gwamna da mataimakisa.

Sanarwar hakan ta fito ne ta bakin mai bawa gwamnan shawarar kan wayar da kan jama'a da sadarwa, Zailani Bappa a ranar Litinin.

A wani labarin daban, 'yan sanda a birnin tarayya Abuja sun kama Ahmad Isah, mai rajin kare hakkin bil adama kuma dan jarida, saboda shararawa wata mari da ake zargi da cin zarafin wata yarinya.

Isah, wanda aka fi sani da 'Ordinary President' ya dade yana gabatar da wani shirin rediyo da talabijin mai suna "Brektet Family".

Al'umma sun yi korafi a kansa ne bayan an gan shi cikin wani faifn bidiyo da BBC Africa Eye ta wallafa yana marin wata mata da ake zargin da cinnawa yar dan uwanta wuta a kai kan zarginta da maita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164