Yanzu-Yanzu: Gwamnati Ta Dakatar Da Shafin Twitter a Nigeria

Yanzu-Yanzu: Gwamnati Ta Dakatar Da Shafin Twitter a Nigeria

- Gwamnatin Nigeria ta dakatar da shafin dandalin sada zumunta na Twitter a kasar

- Lai Mohammed, ministan labarai da al'adu na Nigeria ne ya bada sanarwar a ranar Juma'a

- Gwamnatin Nigeria ta ce ta dakatar da Twitter ne kan zarginta da bada damar tada zaune tsaye a kasar

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shafin dandalin sada zumunta na Twitter a Nigeria kamar yadda gwamnatin ta sanar a shafin ma'aikatar Labarai da al'adu a Twitter.

Ministan sadarwa da al'adu, Lai Mohammed ne ya sanar da dakatarwa a ranar Juma'a a Abuja, yana mai cewa ana amfani da shafin wurin aikata abubuwa da ke barazana ga hadin kan Nigeria.

Ministan ya kuma ce gwamnatin tarayya ta umurci Hukumar Kula da Kafafen Watsa Labarai, NBC, ta fara aikin bada lasisi ga dukkan dandalin sada zumunta ake amfani da su a kasar.

DUBA WANNAN: Da Ɗuminsa: 'Yan Bindiga Sun Sace Wani Ɗan Kasuwa a Kano

Yanzu-Yanzu: Gwamnati Ta Dakatar da Shafin Twitter a Nigeria
Yanzu-Yanzu: Gwamnati Ta Dakatar da Shafin Twitter a Nigeria
Asali: Original

Legit.ng ta ruwaito cewa gwamnatin Nigeria ta fara sa-in-sa da Twitter bayan goge wani sashi na rubutu da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi inda ya gargadi mambobin haramtaciyyar kungiyar masu neman kafa kasar Biafra, IPOB, su dena lalata kayan kasa.

Da ya ke martani kan goge rubutun na Buhari a ranar Laraba, Ministan Labarai da al'adu ya ce bai san dalilin da yasa shafin na Twitter bai goge rubutun da shugaban IPOB Nnamdi Kanu da masu goyon bayansa ke yi ba na tada zaune tsaye.

KU KARANTA: Matawalle Ya Sauke Dukkan Ciyamomi Da Kansiloli a Jihar Zamfara

Mr Mohammed ya ce: "Twitter na da dokokinta; ba dokar duniya bane. Idan Shugaban akwai abin da ya bata wa shugaban kasa rai a ko ina, yana da ikon bayyana ra'ayinsa.

"Mu dena misalta abu biyu da ke banbanci. Idan an haramta kungiya, tana da banbanci da kungiyar da ba a haramta ba."

"Shugaban kasa na da ikon nuna bacin ransa game da duk wata kungiya da ke umurta mambobinta su kashe yan sanda, su kai hari gidajen gyaran hali, su kashe gandirebobi, Me yasa ake nuna wariyya?.

"Ban taba ganin idan a duniya kungiya musamman wadda aka haramta ke umurtar mambobinta su kaiwa gwamnati, yan sanda, da sojoji hari kuma a kyalle ta.

"Babu yadda za a yi ka halasta maganganu na umurnin a kashe yan sanda ko duk wani wanda ra'ayin ku bai zo daya ba."

A wani labarin daban, Hukumar Yaki Da Hana Safarar Miyagun Kwayoyi na Kasa, NDLEA, ta ce ta kama wasu mutane da ake zargi da safararmiyagun kwayoyi a birnin tarayya Abuja, The Cable ta ruwaito.

Femi Babafemi, kakakin NDLEA, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi ya ce an kama su ne sakamakon samamen da hukumar ta yi cikin wannan makon.

Cikin wanda aka kama akwai wata Ese Patrick da ake zargi na siyar da miyagun kwayoyi a dandalin Instagram.

Asali: Legit.ng

Online view pixel