Yanzu-Yanzu: Ƴan Bindiga Sun Kashe Manoma 12, Sun Jikkata wasu 9 a Zamfara

Yanzu-Yanzu: Ƴan Bindiga Sun Kashe Manoma 12, Sun Jikkata wasu 9 a Zamfara

- Yan bindiga sun kai hari a kananan hukumomin Magami da Bayani a jihar Zamfara

- Yan bindigan sun kashe mutane 12 sannan sun raunata wasu mutane tara a yayin harin

- Mai magana da yawun yan sandan jihar ya tabbatar da harin inda ya ce an tura jami'an tsaro

Rahotan da muka samu daga TVC News na cewa wasu yan bindiga sun hallaka manoma 12 tare da raunata wasu tara a kananan hukumomin Magami da Bayani a jihar Zamfara.

Yan bindigan sun kuma sace dabobi da wasu kayayyaki masu muhimmanci da a yanzu ba a tabbatar da adadinsu ba.

Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Kashe Manoma 12, Sun Jikkata wasu 9 a Zamfara
Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Kashe Manoma 12, Sun Jikkata wasu 9 a Zamfara
Asali: Original

Channels TV ta ruwaito cewa yan bindigan sun kai harin ne a lokacin da manoman da aiki a gonakinsu suna kokarin sharar gona domin shirin aikin daminan bana.

DUBA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Gwamnati Ta Dakatar Da Shafin Twitter a Nigeria

An kuma ruwaito cewa an birne mutanen 12 da aka kashe bisa koyarwa addinin musulunci yayin da wadanda suka rasu suna asibiti suna karbar magani.

A wani harin daban, kimanin mutane goma ne aka kashe yayin da aka sace dabobi da yawa yayin da yan bindiga suka kai hari a kauyukan Bardi da Girkau a karamar hukumar Anka.

A cewar wani majiya a Anka, yan bindigan sun kutsa garin ne misalin karfe 9 na daren ranar Alhamis suka fara harbe-harbe inda suka kashe mutane shida a Bardi sannan wasu hudu a Girkau.

KU KARANTA: Da Ɗumi-Ɗumi: Hatsarin Jirgin Ruwa Ya Kashe Mutum 13 a Sokoto

Yan bindigan sun kuma kona babur guda daya suka sace guda biyu.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Zamfara SP Shehu Mohammed ya ce an tura jami'ai garuruwan da abin ya faru kuma ana kokarin gano wadanda suka kai harin domin su girbi abin da suka shuka.

A wani labarin daban, Hukumar Yaki Da Hana Safarar Miyagun Kwayoyi na Kasa, NDLEA, ta ce ta kama wasu mutane da ake zargi da safararmiyagun kwayoyi a birnin tarayya Abuja, The Cable ta ruwaito.

Femi Babafemi, kakakin NDLEA, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi ya ce an kama su ne sakamakon samamen da hukumar ta yi cikin wannan makon.

Cikin wanda aka kama akwai wata Ese Patrick da ake zargi na siyar da miyagun kwayoyi a dandalin Instagram.

Asali: Legit.ng

Online view pixel