Da Ɗumi-Ɗumi: Hatsarin Jirgin Ruwa Ya Kashe Mutum 13 a Sokoto

Da Ɗumi-Ɗumi: Hatsarin Jirgin Ruwa Ya Kashe Mutum 13 a Sokoto

- Hatsarin jirgin ruwa ya yi sanadin rasuwar mutane 13 a karamar hukumar Shagari, jihar Sokoto

- Aliyu Dantine Shagari, shugaban karamar hukumar ya ce mutum takwas cikin wadanda suka rasu matan aure ne yayin da sauran yara ne da maza

- Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto, a safiyar yau Juma'a ya ziyarci garin da abin ya faru domin jajanta musu

Mutane 13 cikinsu har da mata da kananan yara sun riga mu gidan gaskiya sakamakon hatsarin jirgin ruwa da ya faru a karamar hukumar Shagari na jihar Sokoto a ranar Alhamis, rahoton Daily Trust.

Wadanda abin ya shafa sun fito ne daga Doruwa suna kan hanyarsu ta zuwa Dinga a yayin da jirgin ya kife.

Da Dumi-Dumi: Hatsarin Jirgin Ruwa Ya Kashe Mutum 13 a Sokoto
Da Dumi-Dumi: Hatsarin Jirgin Ruwa Ya Kashe Mutum 13 a Sokoto. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Karin Bayani: Sojan Da Ya Bindige Jami'an Kwastam Har Lahira a Legas Ya Kashe Kansa

Da ya ke tabbatar da afkuwar lamarin, shugaban karamar hukumar, Alhajo Aliyu Dantine Shagari, ya ce mutum takwas cikin wadanda suka rasu matan aure ne yayin da sauran yara ne da maza.

Ya ce akwai yiwuwar an yi wa jirgin ruwan yawa ne.

Ya ce, "Amma akwai wasu abubuwa da ke janyo hatsarin jirgin ruwa kamar iska mai karfi. Har yanzu muna cigaba da bincike a kan abin da ya yi sanadin hatsarin jirgin ruwan."

Ya bayyana cewa an ciro dukkan gawarwakin wadanda suka rasu an kuma yi musu jana'iza bisa koyarwar addinin musulunci.

TVC ta ruwaito cewa gwamann jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, a safiyar ranar Juma'a ya ziyarci kauyen domin jajantawa iyalai da mutanen garin da abin ya shafa.

Rahotanni sun ce an ceto mutane bakwai cikin wadanda suke cikin jirgin ruwan yayin da hatsarin ya afku.

KU KARANTA: Masu Garkuwa Da Ƴan Bindiga Sun Ragu Saboda NIN, In Ji Pantami

Ya ce run rasa rayyukan mutane shida a wani hatsarin jirgin ruwa makamancin wannan a shekarar 2020.

A wani labarin daban, daliban makarantun sakandare a jihar Kano sun yi kira ga gwamnatin jihar ta samarwa dalibai mata audugan mata kamar yadda ta ke samar da littafan karatu kyauta, Vanguard ta ruwaito.

Daliban sun koka da cewa yan mata da yawa ba su da kudin siyan audugan matan, don haka suke rokon gwamnatin ta taimaka musu domin su samu su rika tsaftace kansu.

Sun yi wannan rokon ne yayin wani taron wayar da kai na kwana daya da aka yi kan tsaftar mata da jiki da Kungiyar Yan Jarida Masu Rahoto Kan Bangaren Lafiyar Mata reshen jihar Kano suka shirya don bikin ranar Al'adar Mata Ta Duniya na 2021'

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel