Har yanzu gwamnati bata tuntubemu ba, Hukumar makarantar da aka sace yara156
- Shugaban makarantar Islamiyyar da aka sace dalibanta a jihar Neja ya koka da halin ko in kula da gwamnati ta nuna musu
- Alhaji Abubakar Hassan yace har yanzu babu wanda ya tuntubesu daga gwamnatin jihar Neja kan batan daliban
- Ya ce tuni masu garkuwa da mutanen sun tuntubi hukumar makarantar inda suka bukaci naira miliyan 100 na kudin fansa
Alhaji Abubakar Hassan, mamallakin Islamiyyar Salihu Tanko dake garin Tegina a karamar hukumar Rafi ta jihar Neja, ya ce har yanzu gwamnati bata tuntubi hukumar makarantar ba saboda sace daliban da aka yi.
Daily Trust ta ruwaito yadda aka sace wasu daliban makarantar islamiyya a cikin ranakun karshen mako.
A wani sakon murya da aka turawa manema labarai a ranar Laraba, Alhassan yace masu garkuwa da mutanen sun tuntubesu inda suka bukaci kudin fansa har naira miliyan dari.
KU KARANTA: Borno, Adamawa, Yobe da wasu Jihohi 14 masu matukar hatsari a Najeriya
KU KARANTA: EFCC ta cigaba da garkame katafaren gidajen hadimin NSA Monguno a Abuja
"Har yanzu gwamnati bata shiga cikin lamarin ba. Sakataren gwamnatin jihar ya tuntubemu ta bakin matarsa saboda muna da alaka da ita. Ta kira ni kuma ta mika wayar ga mijinta wanda yace suna addu'ar dawowar yaran kuma har a yanzu bai zo mana jaje ba," yace.
Ya kara da cewa yayi kokarin samun shugaban karamar hukumar amma ya sanar da cewa yana wasu 'yan kokari ne.
A daya bangaren, gwamnatin jihar tace tana dukkan kokarin da ya dace wajen ganin an sako yaran makarantar cikin koshin lafiya.
A wani labari na daban, Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya umarci dukkan mazauna jihar da su mika makaman da suka mallaka ba bisa ka'ida ba ga hukumar 'yan sanda mafi kusa dasu a cikin kwanaki bakwai kacal.
Gwamnan ya bada wannan umarnin ne yayin saka hannu a wata takardar shela ga dukkan jihar Zamfara, kamar yadda hadiminsa a harkar yada labarai, Zailani Bappa ya sanar a ranar Laraba.
Kamar yadda takardar ta nuna, umarnin ya biyo bayan umarnin da shugaban kasa ya bada na harbe duk wanda aka kama da makamai ba bisa ka'ida ba a take, Daily Nigerian ta ruwaito.
Asali: Legit.ng