Matawalle ya ba Zamfarawa wa'adin kwana 7 su mika makaman da suka mallaka

Matawalle ya ba Zamfarawa wa'adin kwana 7 su mika makaman da suka mallaka

- Gwamnan Zamfara, ya bukaci mazauna jihar da su mika dukkan makaman da suka mallaka ba bisa ka'ida ba ga 'yan sanda

- Matawalle ya bada wa'adin kwanaki bakwai ga mazauna jihar wadanda suka mallaka makamai ba bisa ka'ida ba

- Ya umarci jami'an tsaro da su harbi duk wanda suka kama da makami ba bisa ka'ida ba kamar yadda Buhari ya umarta

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya umarci dukkan mazauna jihar da su mika makaman da suka mallaka ba bisa ka'ida ba ga hukumar 'yan sanda mafi kusa dasu a cikin kwanaki bakwai kacal.

Gwamnan ya bada wannan umarnin ne yayin saka hannu a wata takardar shela ga dukkan jihar Zamfara, kamar yadda hadiminsa a harkar yada labarai, Zailani Bappa ya sanar a ranar Laraba.

Kamar yadda takardar ta nuna, umarnin ya biyo bayan umarnin da shugaban kasa ya bada na harbe duk wanda aka kama da makamai ba bisa ka'ida ba a take, Daily Nigerian ta ruwaito.

KU KARANTA: An gano hatsabibiyar kungiyar 'yan bindigan da suka sace yaran Islamiyya a Neja

Matawalle ya ba Zamfarawa wa'adin kwana 7 su mika makaman da suka mallaka
Matawalle ya ba Zamfarawa wa'adin kwana 7 su mika makaman da suka mallaka. Hoto daga @daily_nigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Fusatattun matasa sun kori basarake daga fadarsa bayan mutuwar dan sanda a yankin

Takardar ta ce: "Domin tabbatar da karfin ikon da nake da shi, ni Dakta Bello Mohammed, ina bada wadannan umarnin.

"Dukkan makamai dake hannun jama'ar jihar Zamfara ba bisa ka'ida ba, a mika su ga ofishin 'yan sanda mafi kusa a cikin kwanaki bakwai daga ganin wannan sanarwan," takardar ta sanar da hakan.

Bappa ya kara da cewa, gwamnan yayi kira ga mazauna jihar da su kasance masu kiyaye doka domin samun damar shawo kan matsalar tsaro a jihar.

A wani labari na daban, gwamnan jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle, ya sallami dukkan kwamishinoninsa da masu mukaman siyasa na jihar.

Kamar yadda takardar da mai bashi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Zailani Bappa ya fitar a ranar Litinin ta nuna, gwamnan ya bukaci dukkan kwamishinoni da masu mukaman siyasa na jihar da su koma gida su huta.

Kamar yadda wasikar da Zailani Bappa ya wallafa a shafinsa na Facebook ta bayyana, gwamnan yace wannan sallamar bata shafi duk wata hukumar da kundun tsarin mulkin kasar Najeriya ya kafa ba a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel