Borno, Adamawa, Yobe da wasu Jihohi 14 masu matukar hatsari a Najeriya

Borno, Adamawa, Yobe da wasu Jihohi 14 masu matukar hatsari a Najeriya

- Sakamakon hauhawar rashin tsaro a kasar nan, akwai jihohin da aka ware a matsayin masu matukar hatsari a Najeriya

- An shawarci matafiya da su kiyayi jihohin Borno, Adamawa da Yobe saboda sun fi ko ina hatsari a Najeriya

- Kamar yadda rahoton ya nuna, babu jiha a Najeriya da za a iya cewa matafiya zasu iya zuwa ba tare da wata fargaba ba

Jihohi uku na yankin arewa maso gabas sune aka bayyana a matsayin cibiyar ta'addanci na Najeriya. Adamawa, Borno da Yobe sune jihohin da suka fi dukkan jihohi hatsari a kasar nan.

Akwai sauran jihohi 14 da suka fada cikin wannan rukunin na mafi hatsari kamar yadda wani kamfanin tsaro mai zaman kansa, PR24 ya fitar kuma THISDAY ta samu a ranar Litinin.

Sauran jihohi 14 masu tarin hatsari da aka ruwaito sun hada da: Bayelsa, Ebonyi, Delta, Benue, Enugu, Gombe, Imo, Jigawa, Kaduna, Katsina, Filato, Sakkwato, Taraba da Zamfara.

KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun kashe babban jami'in hukumar kula da shige da fice

Borno, Adamawa, Yobe da sauran Jihohi 14 masu matukar hatsari a Najeriya
Borno, Adamawa, Yobe da sauran Jihohi 14 masu matukar hatsari a Najeriya. Hoto daga thisdaylive.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Abu mai Fashewa ya Tashi da Sojojin Najeriya, 7 sun Sheka Lahira a Borno

Yayin da babu jiha a Najeriya da ta shiga sahun jihohi masu tsaro, jihohin Abia, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Cross Rive, Edo, Ekiti, Kano, Kogi, Kwara, Nasarawa, Niger, Ogun, Ondo, Osun, Oyo, Ribas da Abuja sune matsakaita a fannin tsaro.

Kamar yadda rahoton ya nuna, Legas ce kadai jihar da ake ganin yuwuwar rashin tsaro wanda ya nuna cewa idan aka gujewa rikici komai zai daidaita.

Rahoton ya nuna cewa babu jihar da za a iya cewa tana da tsaro kuma matafiya zasu iya zuwa ba tare da wata fargaba ba.

A wani labari na daban, Kungiyar 'yan bindiga da suka shirya sace 'yan matan makarantar sakandare ta Jangebe dake jihar Zamfara a farkon shekarar nan, sune ke da alhakin kwashe daliban Islamiyya a Tegina dake karamar hukumar Rafi ta jihar Neja, Daily Trust ta tabbatar.

Mambobin kungiyar sun kwashe dalibai masu yawa daga jihar Neja a ranar Asabar da ta gabata, wata majiya mai karfi ta tsaro ta sanar da Daily Trust, duk da babu dalilin wannan aika-aikar har yanzu.

Gagararriyar kungiyar 'yan bindigan da ta samu jagorancin Na-Sanda, sun dade suna ta'asa a dajin Jangebe dake karamar hukumarr Talatan Mafara ta jihar Zamfara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel