EFCC ta cigaba da garkame katafaren gidajen hadimin NSA Monguno a Abuja

EFCC ta cigaba da garkame katafaren gidajen hadimin NSA Monguno a Abuja

- Hukumar yaki da rashawa ta cigaba da kwace gidajen Birgediya Janar Jafaru Mohammed, hadimi kumsa shakikin NSA Monguno

- An gano cewa yayin da jami'an EFCC suke je garkame gidajen a Lokogoma, an turo sojoji inda suka dinga harbinsu

- Tuntuni aka zargi Babagana Monguno da baiwa sojan kariya saboda tsoron koda akwai kadarorinsa dake cikin harkallar

Hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta garkamen karin gidaje wadanda ake zargin mallakin Birgediya Janar Jafaru Mohammed ne.

Birgediya Janar Jafaru Mohammed shine daraktan kudi na ofishin mai bada shawara kan tsaron kasa, Babagana Monguno.

Tun farkon binciken, majiyoyi sun ce NSA ya dinga amfani da kujerarsa wurin hana bincike a kan tsoron wasu daga cikin kadarorin biliyoyin nairan zasu iya zama masu alaka da shi.

Daily Nigerian ta tattaro cewa, a ranar Laraba, 27 ga watan Mayu, sojoji da ake zargin sun bi umarnin NSA ne sun dinga harbin jami'an EFCC da suka je rubutu tare da garkame gidajen dake rukunin gidaje na Sun City, Lokogoma, Abuja.

KU KARANTA: Abu mai Fashewa ya Tashi da Sojojin Najeriya, 7 sun Sheka Lahira a Borno

EFCC ta cigaba da garkame katafaren gidajen hadimin NSA Monguno a Abuja
EFCC ta cigaba da garkame katafaren gidajen hadimin NSA Monguno a Abuja. Hoto daga @daily_nigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Gagarumar Gobara ta lashe fitaccen katafaren otal a Ikeja, Legas

Majiyoyi sun sanar da cewa EFCC ta saka wa sama da gidaje 12 makin kwacewa a jihar Kano a ranar Litinin wadanda ke da alaka da sojan.

Idan zamu tuna, EFCC ta samu dama daga wata kotun tarayya dake Abuja a eanae 11 ga watan Maris 2021 na kuma ta kwace wasu gidaje takwas mallakin soja.

A wata kara mai lamba FHC/ABJ/CS/007/2021, mai shari'a Folashade Agunbanjo ya bada umarnin kwace gidaje takwas da suke da laka da Mohammed, wanda hadimi ne kum babban makusanci ga NSA, manjo janar Babagana Monguno.

A wani labari na daban, kungiyar 'yan bindiga da suka shirya sace 'yan matan makarantar sakandare ta Jangebe dake jihar Zamfara a farkon shekarar nan, sune ke da alhakin kwashe daliban Islamiyya a Tegina dake karamar hukumar Rafi ta jihar Neja, Daily Trust ta tabbatar.

Mambobin kungiyar sun kwashe dalibai masu yawa daga jihar Neja a ranar Asabar da ta gabata, wata majiya mai karfi ta tsaro ta sanar da Daily Trust, duk da babu dalilin wannan aika-aikar har yanzu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel