'Yan bindiga sun sake halaka mutane a ƙananan hukumomi biyu a Kaduna

'Yan bindiga sun sake halaka mutane a ƙananan hukumomi biyu a Kaduna

- Yan bindiga sun sake kai hare-hare a ƙananan hukumomin Giwa da Birnin Gwari a jihar Kaduna

- Yan bindigan sun halaka wani bawan Allah mai suna Yusuffa Karami a Birnin Gwari sannan suka kashe Fanyo Bello a Giwa

- Wannan hare-haren na zuwa ne bayan harin da wasu yan bindigan suka kai a Goska a ƙaramar hukumar Jema'a suka halaka mutum hudu

Ƴan bindiga sun halaka mutane biyu a ƙananan hukumomin Giwa da Birnin Gwari na jihar Kaduna a wani sabin hari da suka kai.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Mr Samuel Aruwan ne ya sanar da hakan a ranar Talata, Channels Tv ta ruwaito.

Yan Bindiga Sun Sake Kashe Mutane Biyu a Sabon Harin Da Suka Kai Kaduna
Yan Bindiga Sun Sake Kashe Mutane Biyu a Sabon Harin Da Suka Kai Kaduna. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: An Kashe Sufetan Ƴan Sanda Da Wasu Mutane Shida a Ƙauyen Katsina

A cewar kwamishinan, yan bindigan sun kashe wani Yusuffa Karami a Maikulu a ƙaramar hukumar Birnin Gwari, yayin da aka tabbatar da mutuwar wani Fanyo Bello sakamakon harbinsa da bindiga da yan bindiga suka yi a Unguwan Maikuzanniya a ƙaramar hukumar Giwa a safiyar yau.

Hukumomin tsaro sun kuma tabbatar da cewa wata dattijuwa ta ɗauki ranta da kanta a Gonon Rogo a ƙaramar hukumar Kajuru na jihar.

Rahotanni sun ce dattijuwar ta yi amfani da igiya ne ta nada a wuyanta a cikin ɗaki har ta ce ga garinku. A halin yanzu ba a san dalilin da yasa ta aikata hakan ba.

KU KARANTA: Sabon Salo: 'Yan fashi sun fara zuwa sata gidajen mutane da na'urar POS

Wannan sabbin hare-haren na zuwa ne bayan yan bindiga sun halaka mutane hudu a garin Goska da ke ƙaramar hukumar Jema'a na jihar.

A wani labarin daban, Hukumar Yaki Da Hana Safarar Miyagun Kwayoyi na Kasa, NDLEA, ta ce ta kama wasu mutane da ake zargi da safararmiyagun kwayoyi a birnin tarayya Abuja, The Cable ta ruwaito.

Femi Babafemi, kakakin NDLEA, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi ya ce an kama su ne sakamakon samamen da hukumar ta yi cikin wannan makon.

Cikin wanda aka kama akwai wata Ese Patrick da ake zargi na siyar da miyagun kwayoyi a dandalin Instagram.

Asali: Legit.ng

Online view pixel