An Kashe Sufetan Ƴan Sanda Da Wasu Mutane Shida a Ƙauyen Katsina
- Rayyuka bakwai sun salwanta sakamakon harin da ƴan bindiga suka kai ƙauyen Zandam a Katsina
- Cikin wadanda suka mutu akwai ɗan sanda daya, mazauna garin uku da ƴan bindiga uku
- Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar SP Gambo Isah ya tabbatar da afkuwar harin
An kashe mutane bakwai cikinsu har da dan sanda mai muƙamin sufeta yayin da yan bindiga suka kai hari ƙauyen Zandam da ke ƙaramar hukumar Jibia ta jihar Katsina da yammacin ranar Litinin.
The Punch ta ruwaito cewa cikin wadanda aka kashe akwai mazauna ƙauyen uku da ƴan bindiga uku.
Mai magana da yawun rundunar yansandan jihar, SP Gambo Isah, wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin a ranar Talata ya ce biyar cikin mutanen garin sun jikkata.
DUBA WANNAN: An Bayyana Ranar Da Gwamnan Zamfara Matawalle Zai Koma Jam'iyyar APC
An ruwaito cewa yan bindigan da suka kutsa garin misalin ƙarfe 5 na yammacin ranar Litinin sun kashe mutane uku dukkansu maza.
Sun kuma raunata mutane biyar sannan suka kona wani kango da ake amfani da shi a matsayin wurin duba marasa lafiya a kauyen.
Yan sandan da aka tura kai dauki a ƙauyen sunyi gumurzu sosai da yan bindigan inda suka kashe uku cikinsu da kuma ɗan sanda daya mai muƙamin sufeta ya rasu.
Kakakin yan sandan ya ce, "A ranar 31/5/2021 misalin ƙarfe 5 na yamma, Yan bindiga da dama ɗauke da muggan makamai, kan babura sun afka kauyen Zandam, ƙaramar hukumar Jibia na jihar.
KU KARANTA: Za a Fara Bawa Malaman Makarantun Allo Shaidar Karatu Ta ‘NCE’ a Kaduna
"Sunyi musayar wuta da yan sandan da aka tura ƙauyen. A wurin an gano yan bindigan sun kashe mutum uku maza (mazauna ƙauyen) yayin da biyar suka jikkata. Tawagar ta yi nasarar bindige uku cikin ƴan bindigan. Sufeta na ƴan sanda daya ya rasu sakamakon gumurzun. Ƴan bindiga sun kona wani kango da ake amfani da shi matsayin asibiti.
"An tura karin yan sanda zuwa garin an bawa wadanda suka jikkata taimakon gaggawa an kai su babban asibitin garin. An fara bincike da nufin gano maharan da suka tsere."
A wani labarin daban, Hukumar Yaki Da Hana Safarar Miyagun Kwayoyi na Kasa, NDLEA, ta ce ta kama wasu mutane da ake zargi da safararmiyagun kwayoyi a birnin tarayya Abuja, The Cable ta ruwaito.
Femi Babafemi, kakakin NDLEA, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi ya ce an kama su ne sakamakon samamen da hukumar ta yi cikin wannan makon.
Cikin wanda aka kama akwai wata Ese Patrick da ake zargi na siyar da miyagun kwayoyi a dandalin Instagram.
Asali: Legit.ng