Da Duminsa: An Bindige Minista a Uganda, An Kashe Ƴarsa Da Mai Tsaronsa

Da Duminsa: An Bindige Minista a Uganda, An Kashe Ƴarsa Da Mai Tsaronsa

- Yan bindiga sun kaiwa ministan sufurin kasar Uganda, Janar Wamala hari a Kampala

- Yayin harin, yan bindigan da suka taho kan babura sun halaka yar ministan da mai tsaronsa

- Gwamnatin jihar Uganda ta tabbatar da harin tana mai cewa Wamala yana asibiti kuma an fara bincike

An harbi ministan sufuri na kasar Uganda, wanda a baya ke jagorantar sojojin kasar, a wani harin da aka kai masa a ranar Talata inda aka kashe yarsa da mai tsaronsa, kamar yadda majiyar gwamnatin kasar ta sanar.

Ministan, Janar Edward Katumba Wamala, wanda ya rike mukamin babban hafsan tsaron kasar daga 2013 zuwa 2017, ya ci karo da maharan ne a Kampala, a cewar mai magana da yawun gwanati, Chris Baryomunsi.

Da Duminsa: An Bindige Minista a Uganda, An Kashe Ƴarsa da Mai Tsaronsa
Da Duminsa: An Bindige Minista a Uganda, An Kashe Ƴarsa da Mai Tsaronsa. Hoto: @GenWamala
Asali: Twitter

KU KARANTA: Za a Fara Bawa Malaman Makarantun Allo Shaidar Karatu Ta ‘NCE’ a Kaduna

"An yi yunkurin kashe Wamala a safiyar yau ... An bindige yarsa da mai tsaronsa kuma sun mutu nan take," Baryomunsi ya shaidawa AFP a ranar Talata.

"An garzaya da Janar Katumba zuwa asibiti da raunin harsashi a cikinsu kuma ana masa magani, masu bincike sun isa wurin da abin ya faru," ya kara da cewa.

"Akwai yiwuwar wannan kisar gilla aka yi niyyar yi amma bincike zai bayyana ainihin dalilin kai harin."

Wasu da abin ya faru a idonsu sun shaidawa gidajen talabijin na kasar cewa wasu mutane hudu da suka rufe fuskokinsu a kan babura ne suka bude wa motar Wamala wuta.

KU KARANTA: Da Duminsa: Buhari Ya Cire Shugaban NEMA, Ya Maye Gurbinsa Da Habib

Hotuna da aka dauka sun nuna alamun yadda harsashi ya ratsa jikin motar mai lamba launin kore na gwamnatin kasar.

Harin na ranar Talata shine na baya-baya da mahara a kan babura ke kaiwa manyan mutane a babban birnin na Uganda.

A Yunin 2018, an halaka Ibrahim Abiriga, wani babban dan siyasa a jam'iyyar National Resistance Movement party a yanayi mai kama da wannan.

A wani labarin daban, Hukumar Yaki Da Hana Safarar Miyagun Kwayoyi na Kasa, NDLEA, ta ce ta kama wasu mutane da ake zargi da safararmiyagun kwayoyi a birnin tarayya Abuja, The Cable ta ruwaito.

Femi Babafemi, kakakin NDLEA, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi ya ce an kama su ne sakamakon samamen da hukumar ta yi cikin wannan makon.

Cikin wanda aka kama akwai wata Ese Patrick da ake zargi na siyar da miyagun kwayoyi a dandalin Instagram.

Asali: Legit.ng

Online view pixel