Da Duminsa: Buhari Ya Cire Shugaban NEMA, Ya Maye Gurbinsa Da Habib

Da Duminsa: Buhari Ya Cire Shugaban NEMA, Ya Maye Gurbinsa Da Habib

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin Ahmed Mustapha Habib a matsayin sabon shugaban hukumar bada agajin gaggawa na kasa, NEMA, domin mayar da martanin AVM Muhammad (mai ritaya).

Bayan cire shi, an nada Mohammed a matsayin shugaban kwamitin hukuma ta mutane masu manyan shekaru 'National Senior Citizens Centre."

Da Duminsa: Buhari Ya Cire Shugaban NEMA, Ya Maye Gurbinsa Da Habib
Da Duminsa: Buhari Ya Cire Shugaban NEMA, Ya Maye Gurbinsa Da Habib. Hoto: @daily_nigerian
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Rayuka 12 Sun Salwanta a Sabin Hare-Haren Da Aka Kai a Ado

A cikin sanarwar da ya fitar, mai magana da yawun shugaban kasa Garba Shehu ya ce Buhari ya amince a fara aiki a cibiyar da mutane masu manyan shekaru bayan kafa kwamitin amintattu mai mambobi 12.

Mai magana da yawun shugaban kasan ya ce kafa wannan hukumar ya dace da sashi na 16 (2) (d) na kundin tsarin mulkin Nigeria da aka yi wa kwaskwarima wanda ya dora wa kasar alhakin samar da ababen more rayuwa don inganta rayyukan dattijai.

KU KARANTA: Rashin Tsaro: Masu Zanga-Zanga Sun Rufe Manyan Tituna a Zamfara

AVM Muhammad shine tsohon shugaban hukumar bada agaji ta kasa wato NEMA.

"An yi dokar National Senior Citizens Centre ne tun a shekarar 2017 domin kulawa da bukatun dattijai (wadanda suka dara shekaru 70) a kasar.

"Domin cimma wannan manufar mai muhimmanci an nada wasu mutane masu gaskiya da rikon amana daga ma'aikatu da hukumomi a kwamitin amintattu na hukumar.

"Shugaba Buhari ya nada AVM M.A. Muhammad (mai murabus) a matsayin shugaban kwamitin, Mansur Kuliya shi ke wakiltar Ma'aikatar Jin Kai da Cigaban Al'umma da Kare Afkuwar Bala'i; Dr Chris Osa Isopunwu ke wakiltar Ma'aikatar Lafiya ta Tarayya; Mr Umar Abdullahi Utono ke wakiltar Ma'aikatar Ayyuka Da Gidaje; da Dr John Olushola Magbadelo da ke wakiltar Ma'aikatar Kwadago.

"Sauran mambobi sun hada Mrs Bitrus Kimde mai wakiltar Ma'aikatar Mata ta Tarayya; Mr Sani Ibrahim Mustapha mai wakiltar hukumar kula da fansho ta PTAD; Farfesa Usman Ahmed mai wakiltar Kungiyar Dattijai ta Nigeria; Arc. Mrs Victoria Onu ke wakiltar Hadakar kungiyoyi masu kare hakkokin dattijai (CORSOPIN) da wasu masu ruwa da tsaki Dr Dorothy Nwodo, Farfesa Mohammed Mustapha Namadi da Dr Emem Omokaro da za su yi aiki matsayin manyan direktoci," a cewar sanarwar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164