Rashin Tsaro: Masu Zanga-Zanga Sun Rufe Manyan Tituna a Zamfara

Rashin Tsaro: Masu Zanga-Zanga Sun Rufe Manyan Tituna a Zamfara

- Daruruwan mutane sun fita yin zanga-zanga a Zamfara domin nuna bacin ransu kan hare-haren yan bindiga

- Masu zanga-zangar sun rufe manyan tituna a jihar inda suka rika kone-kone domin janyo hankalin mahukunta

- Wani daga cikin masu zanga-zangan ya ce sun gaji da yadda yan bindigan ke kai musu hare-hare suna kisa ba tare da jami'an tsaro na daukan mataki ba

Mutanen gari a jihar Zamfara a karamar hukumar Kaura Namoda sun rufe manyan tituna a jihar a ranar Litinin suna zanga-zanga game da yawan hare-hare a jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Masu zanga-zanga da suka raba kansu gida shida a kan babban titin Gusau-Kaura Namoda sun kuna wuta a kan titi a Sabon Garin Kaura Namado, Guiwa Junction, Fegin magaji, Kuryar Madaro Junction, Maguru, Kasuwar Daji da Kyambarawa.

DUBA WANNAN: Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Kashe Ahmed Gulak, Tsohon Hadimin Goodluck Jonathan

Rashin Tsaro: Masu Zanga-Zanga Sun Rufe Manyan Tituna Zamfara
Rashin Tsaro: Masu Zanga-Zanga Sun Rufe Manyan Tituna Zamfara. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

A cewar Sahara Reporters, wasu masu zanga-zangar sun tare matifya kimanin 500 a babban titin kurya.

A baya bayan nan, an yi ta kai hare-hare a jihar ta Zamfara da ake zargin yan bindiga ne ke kaiwa.

A ranar Juma'a da ta gabata, wasu masu zanga-zangan sun tafi fadar sarkin Zurmi da gawarwakin wasu mutane da yan bindiga suka kashe.

Wasu daga cikin masu zanga-zangan sun ce sun gaji da yadda yan bindigan ke kai musu hare-hare ba tare da yan jami'an tsaro na kawo musu dauki ba.

KU KARANTA: Rayuka 12 Sun Salwanta a Sabin Hare-Haren Da Aka Kai a Ado

"Ana kashe mu kaman beraye. Sai yaushe za mu ga karshen wannan? Akwai wani gari da aka kai hari kwanaki uku a jere kuma babu wanda ya kai musu dauki. Shin mu ba 'yan adam bane? Ya zama dole mahukunta su ji wannan," a cewar daya daga cikin masu zanga-zangan da ya ce sunansa Aminu.

Ba a samu ji ta bakin, SP Muhammad Shehu, mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar ba a lokacin hada wannan rahoton.

A wani labari daban, Ƴan bindiga sun kashe ƴan sa-kai 19 a ƙauyen Yartsakuwa a ƙaramar hukumar Rabah na jihar Sokoto kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wani mazaunin garin, wanda ya yi magana da majiyar Legit.ng a wayar tarho ya ce ƴan sa-kan sun rasa rayukansu ne yayin da suke ƙoƙarin daƙile harin da ƴan bindigan suka kaiwa garin.

Mazaunin garin, da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce yan bindigan sun kai hari ne ƙauyen misalin ƙarfe ɗaya na ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel