Masarautar Lapai Ta Tuɓe Wa Dagaci Rawani a Jihar Niger
- An tsige Abdulqadir Maigari a matsayin dagacin ƙauyen Muye a masarautar Lapai ta jihar Niger
- Sakataren masarautar na Lapai, Ibrahim Sheikh ne ya fitar da sanarwar tsigewan da ta fara aiki a ranar 25 ga watan Mayu
- Sanarwar ta ce an tsige Abdulqadir Maigari ne saboda saɓa wasu dokokin masarautar duk da kuwa an ja masa kunne sau da yawa
Masarautar Lapai a jihar Niger ta tsige dagacin ƙauyen Muye, Abdulqadir Maigari, saboda saɓa dokokin masarautar gargajiya bayan gargadin da aka masa sau da dama.
A cikin sanarwar da ta fitar a ranar Litinin ta bakin sakataren ta, Ibrahim Shiekh, masarautar ta ce dakatarwar za ta fara aiki daga ranar 25 ga watan Mayun 2021, rahoton Channels Television.
DUBA WANNAN: Rayuka 12 Sun Salwanta a Sabin Hare-Haren Da Aka Kai a Ado
Ya yi bayanin cewa masarautar ta rubuta wasika ga Ma'aikatar Ƙananan Hukumomi da Masarautu a ranar 28 ga watan Mayu, tana neman izinin Gwamna Abubakar Bello don tsige Maigari a matsayin dagacin Muye.
A cewar Shiekh, an sanar da shi tsige dagacin ne a wata wasika mai ɗauke da kwanan wata na 29 ga watan Mayu da sa hannun Etsu Lapai, Umar Bago Tafida III.
"Mai martaba, Etsu Lapai kuma shugaban masarautar Lapai ya umurce ni da in sanar da kai cewa an tsige ka matsayin dagacin ƙauyen Muye bisa la'akari da sashi na 80 sakin layi na 2 na dokar ƙananan hukumomin jihar Niger kuma da amincewar mai girma gwamna," in ji wasikar.
KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Kashe Ahmed Gulak, Tsohon Hadimin Goodluck Jonathan
A wani wurin a ƙaramar hukumar Mariga, ƴan bindiga sun kai hari garin Beri a mazabar Bobi.
Yayin harin, sun kashe a kalla mutane 13 ciki har da jami'an tsaro yayin da aka ƙona ofishin ƴan sanda.
A wani labarin daban, 'yan sanda a birnin tarayya Abuja sun kama Ahmad Isah, mai rajin kare hakkin bil adama kuma dan jarida, saboda shararawa wata mari da ake zargi da cin zarafin wata yarinya.
Isah, wanda aka fi sani da 'Ordinary President' ya dade yana gabatar da wani shirin rediyo da talabijin mai suna "Brektet Family".
Al'umma sun yi korafi a kansa ne bayan an gan shi cikin wani faifn bidiyo da BBC Africa Eye ta wallafa yana marin wata mata da ake zargin da cinnawa yar dan uwanta wuta a kai kan zarginta da maita.
Asali: Legit.ng