Yanzu-Yanzu: Buhari Ya Amince Da Kafa Hukuma Ta Musamman Don 'Dattijai' a Nigeria

Yanzu-Yanzu: Buhari Ya Amince Da Kafa Hukuma Ta Musamman Don 'Dattijai' a Nigeria

- Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da kafa hukuma ta musamman don kulawa da bukatun dattijai

- Hadimin shugaban kasa a bangaren sabbin kafafen watsa labarai, Bashir Ahmad ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter

- An kuma nada wasu mutane 12 masu gaskiya da rikon amana a cikin kwamitin amintattu na sabuwar hukumar ta dattijai

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da kafa cibiya ta musamman domin kulawa da batutuwan da suka shafi dattijai a Nigeria mai suna 'National Senior Citizens Centre'.

Mai magana da yawun shugaban kasa Bashir Ahmed ya sanar da cewa an nada Dr Emem Omokaro a matsayin direkta janar na cibiyar.

Yanzu-Yanzu: Buhari ya amince da kafa hukuma ta musamman don 'dattijai' a Nigeria
Yanzu-Yanzu: Buhari ya amince da kafa hukuma ta musamman don 'dattijai' a Nigeria
Asali: Original

DUBA WANNAN: Rashin Tsaro: Masu Zanga-Zanga Sun Rufe Manyan Tituna a Zamfara

Shugaban kasar ya kuma amince da kafa kwamitin amintattu na cibiyar mai mutane 12 inda aka nada AVM M.A. Muhammad (mai murabus) a matsayin shugaban kwamitin.

AVM Muhammad shine tsohon shugaban hukumar bada agaji ta kasa NEMA.

"An yi dokar National Senior Citizens Centre ne tun a shekarar 2017 domin kulawa da bukatun dattijai (wadanda suka dara shekaru 70) a kasar.

"Domin cimma wannan manufar mai muhimmanci an nada wasu mutane masu gaskiya da rikon amana daga ma'aikatu da hukumomi a kwamitin amintattu na hukumar.

"Shugaba Buhari ya nada AVM M.A. Muhammad (mai murabus) a matsayin shugaban kwamitin, Mansur Kuliya shi ke wakiltar Ma'aikatar Jin Kai da Cigaban Al'umma da Kare Afkuwar Bala'i; Dr Chris Osa Isopunwu ke wakiltar Ma'aikatar Lafiya ta Tarayya; Mr Umar Abdullahi Utono ke wakiltar Ma'aikatar Ayyuka Da Gidaje; da Dr John Olushola Magbadelo da ke wakiltar Ma'aikatar Kwadago.

KU KARANTA: An Haramta Shan Taba Sigari a Bainar Jama'a a Jihar Kano

"Sauran mambobi sun hada Mrs Bitrus Kimde mai wakiltar Ma'aikatar Mata ta Tarayya; Mr Sani Ibrahim Mustapha mai wakiltar hukumar kula da fansho ta PTAD; Farfesa Usman Ahmed mai wakiltar Kungiyar Dattijai ta Nigeria; Arc. Mrs Victoria Onu ke wakiltar Hadakar kungiyoyi masu kare hakkokin dattijai (CORSOPIN) da wasu masu ruwa da tsaki Dr Dorothy Nwodo, Farfesa Mohammed Mustapha Namadi da Dr Emem Omokaro da za su yi aiki matsayin manyan direktoci," a cewar sanarwar.

A wani labarin daban, Hukumar Yaki Da Hana Safarar Miyagun Kwayoyi na Kasa, NDLEA, ta ce ta kama wasu mutane da ake zargi da safararmiyagun kwayoyi a birnin tarayya Abuja, The Cable ta ruwaito.

Femi Babafemi, kakakin NDLEA, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi ya ce an kama su ne sakamakon samamen da hukumar ta yi cikin wannan makon.

Cikin wanda aka kama akwai wata Ese Patrick da ake zargi na siyar da miyagun kwayoyi a dandalin Instagram.

Asali: Legit.ng

Online view pixel