An Haramta Shan Taba Sigari a Bainar Jama'a a Jihar Kano
- Gwamnatin jihar Kano ta haramta shan taba cigari a bainar jama'a a fadin jihar
- Kwamishinan lafiya na jihar, Dr Aminu Ibrahim ne ya bada sanarwar hakan a ranar Litinin
- Dr Ibrahim ya kuma ce gwamnatin na Kano na aiki don kafa hukuma da za ta hana siyarwa yara yan kasa da shekaru 18 cigari
Gwamnatin jihar Kano ta hana shan sigari a bainar jama'a domin yaki da annobar cigari a yayin da ake samun kimanin mutane 16,100 da ke mutuwa duk shekara daga matsaloli masu alaka da cigari, Daily Trust ta ruwaito.
A wani mataki na habbaka lafiya da rayuwar al'umma a jihar na Kano, gwamnatin jihar ta ce ta ware kudade da dama domin yaki da cututtuka marasa saurin yaduwa kamar hawan jini, sikila, asma da ciwon huhu masu alaka da shan cigari da sauransu.
DUBA WANNAN: Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Kashe Ahmed Gulak, Tsohon Hadimin Goodluck Jonathan
Yayin taron manema labarai da aka yi a ranar Litinin a Kano domin bikin ranar Yaki da Cigari na Duniya (WNTD), kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dr Aminu Ibrahim Tsanyawa ya ce gwamnatin jihar na aiki tukuru don ganin ta rage adadin masu shan tabar sigari a jihar.
"Muna da doka da ta yi magana takamaime kan hana shan cigaba da bainar jama'a da kuma hana sayarwa yara masu shekaru kasa da 18 cigari. Kazalika, gwamnati za ta cigaba da wayar da kan mutane kan hadarin da ke tattare da shan cigari da dalilin da yasa ya kamata su dena sha," in ji shi.
KU KARANTA: Rayuka 12 Sun Salwanta a Sabin Hare-Haren Da Aka Kai a Ado
Kwamishinan ya kara da cewa a halin yanzu akwai wata doka a gabban majalisar dokokin jihar domin za a kafa hukuma ta 'Hana Yara Shan Miyagun Kwayoyi' a jihar wacce za a daura wa nauyin tabbatar rage yadda mutane ke shan miyagun kwayoyi a jihar.
Tsanyawa ya kara da cewa nan bada dadewa ba gwamnati za ta kafa da za ta yi aiki da masu ruwa da tsaki don rage ta'amulli da miyagun kwayoyi a jihar.
A wani labarin daban, Hukumar Yaki Da Hana Safarar Miyagun Kwayoyi na Kasa, NDLEA, ta ce ta kama wasu mutane da ake zargi da safararmiyagun kwayoyi a birnin tarayya Abuja, The Cable ta ruwaito.
Femi Babafemi, kakakin NDLEA, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi ya ce an kama su ne sakamakon samamen da hukumar ta yi cikin wannan makon.
Cikin wanda aka kama akwai wata Ese Patrick da ake zargi na siyar da miyagun kwayoyi a dandalin Instagram.
Asali: Legit.ng