'Yan Bindiga Sun Bi Dare Sun Kashe Ɗan Hakimi a Gidansa

'Yan Bindiga Sun Bi Dare Sun Kashe Ɗan Hakimi a Gidansa

- Wasu yan bindiga sun kutsa garin Reke sun halaka babban yaron Hakimi a gida cikin dare

- Mai magana da yawun hukumar NSCDC na jihar, Babawale Afolabi ya tabbatar da hakan

- Afolabi ya ce jami'an yan sanda sun tafi da gawar mamacin asibiti sannan an fara bincike kan lamarin

Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kutsa garin Reke, layin Eyenkorin/Afon a karamar hukumar Asa sun kashe wani yaron jagoran jama'a a jihar Kwara, The Nation ta ruwaito.

An ruwaito cewa gungun yan bindigan sun kutsa garin ne misalin karfe biyu na dare suka tafi gidan Alhaji Abdullahi Jimoh, Magajin Garin suka bude wa babban yaronsa mai suna Abiodun wuta.

DUBA WANNAN: Rashin Tsaro: Masu Zanga-Zanga Sun Rufe Manyan Tituna a Zamfara

'Yan Bindiga Sun Halaka Dan Dagacin Kauye a Jihar Kwara
'Yan Bindiga Sun Halaka Dan Dagacin Kauye a Jihar Kwara. Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

Daily Trust ta ruwaito cewa mai magana da yawun hukumar tsaro ta NSCDC a reshen jihar Kwara, Babawale Afolabi ya tabbatar da afkuwar lamarin, yana mai cewa an tafi da gawar marigayin babban asibitin Afon.

Ya ce, "Bayanan da NSCDC ke samu na cewa wasu yan bindiga sun afka garin Reke cikin dare misalin karfe 2 sun tafi gidan magajin kauyen Reke sun kashe dan dagacin kauyen.

KU KARANTA: An Haramta Shan Taba Sigari a Bainar Jama'a a Jihar Kano

"Mutane suna zaman dar-dar yayin da labarin ke bazuwa a cikin gari. Yan sanda na yankin Afon sun tafi da gawarsa zuwa asibiti don yi gwaji."

Ya kara da cewa jami'an NSCDC sun ziyarci wurin da abin ya faru kuma sun fara bincike a kan lamarin.

A wani labarin daban, Hukumar Yaki Da Hana Safarar Miyagun Kwayoyi na Kasa, NDLEA, ta ce ta kama wasu mutane da ake zargi da safararmiyagun kwayoyi a birnin tarayya Abuja, The Cable ta ruwaito.

Femi Babafemi, kakakin NDLEA, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi ya ce an kama su ne sakamakon samamen da hukumar ta yi cikin wannan makon.

Cikin wanda aka kama akwai wata Ese Patrick da ake zargi na siyar da miyagun kwayoyi a dandalin Instagram.

Asali: Legit.ng

Online view pixel