Da duminsa: Mutum 2 sun hallaka, da yawa sun jikkata a zaben APC dake gudana a Legas

Da duminsa: Mutum 2 sun hallaka, da yawa sun jikkata a zaben APC dake gudana a Legas

- An waye gari da rikici a jihar Legas kan zaben fiddan gwanin kananan hukumomi

- Akalla mutum biyu sun rasa rayukansu

- Matasa sun gudanar da zanga-zanga a sakatariyar jam'iyyar

Zaben fidda gwanin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na zaben kananan hukumomi dake gudana ranar Asabar ya bar mutum biyu a mace da kuma wasu dama a jikkace a Surulere.

Mutane da dama sun jikkata a kananan hukumomi irinsu Shomolu, Alimosho, Ejigbo, Ifako Ijaye, dss.

A riwayar Daily Trust, an shiga tashin hankali a fadin jihar kan zaben fiddan gwnain kujerar shugabannin kananan hukumomi 57 da kansiloli 377.

Wasu mambobin jam'iyyar sun zargi yan siyasa da kokarin kakaba musu yan takara.

Abin ya fi tsanani a Surulere inda yan baranda suka ci karensu ba babbaka.

Hakazalika wasu matasa maus bindigogi da muggan makamai sun kaiwa jami'an shirya zabe hari a karamar hukumar Shomolu da Itire-Ikate LCDA.

An tura jami'an yan sanda Sakatariyar APC dake titin Acme gudun kada a kai hari wajen.

KU DUBA: Nan da watan Yuli zamu fara ginin layin dogon Kaduna zuwa Kano, Minista Amaechi

Da duminsa: Mutum 2 sun hallaka, da yawa sun jikkata a zaben APC dake gudana a Legas
Da duminsa: Mutum 2 sun hallaka, da yawa sun jikkata a zaben APC dake gudana a Legas hoto: @phcnstaffnation
Asali: Twitter

DUBA NAN: Kulli yaumin muna ciyar da yan makaranta milyan goma, Hajiya Sadiya

A bangare guda, yan bindiga masu garkuwa da mutane sun sake daliban jami'ar Greenfield bayan sama da wata guda a hannunsu.

Shugaban kungiyar iyayen daliban, Markus Zarmai da wasu sun je tarban tarban inda yan bindigan sukayi alkawarin ajiyesu.

Legit ta tuntubi Kakakin hukumar yan sandan jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, kuma ya tabbatar da wannan labari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel