Kulli yaumin muna ciyar da yan makaranta milyan goma, Hajiya Sadiya

Kulli yaumin muna ciyar da yan makaranta milyan goma, Hajiya Sadiya

- Ministar walwala da jin dadin jama'a ta kaddamar da rabon kayan girki ga ma'aikata

- Gwamnatin Buhari a 2016 ta kaddamar shirin ciyar da daliban makarantun firamare

- Ko da lokacin dokar kulle da ba'a zuwa makaranta, gwamnati tace an rabawa yara abinci a gidajensu

Gwamnatin tarayya a ranar Talata ta sanar da cewa ta samu nasarar ciyar da daliban makaranta milyan goma karkashin shirin ciyar da yan makaranta a fadin tarayya watau NHGSFP.

Ministar tallafi, kula da annoba da jin dadin jama'a, Hajya Sadiya Umar Farouq, ta sanar da hakan a Abuja a bikin kaddamar da shirin rabon kayayyakin girki a Abuja, rahoton Punch

A cewar Minista Sadiya, gwamnatin tarayya ta dauki masu girki sama da 100,000 aiki don yiwa daliban abinci.

Tace: "A yau, mun zo nan don cika alkawarin shugaban kasa na mikawa hukumomin Abuja kayayyakin girki domin amfanin daliban makaranta dake shirin ciyar da yara."

"Manufar wannan shiri shine janyo hankalin yara su fara zuwa makaranta, habaka kiwon lafiyarsu ta abinci mai kyau, inganta aikin noma, da kuma samawa miliyoyin mutan karkara ayyukan yi."

KU KARANTA: Shugaban kasar Mali da Firai Ministansa sun yi murabus

Kulli yaumin muna ciyar da yan makaranta milyan goma, Hajiya Sadiya
Kulli yaumin muna ciyar da yan makaranta milyan goma, Hajiya Sadiya @Sadiya_farouq
Asali: Twitter

DUBA NAN: Gwamna Bala Muhammad ya halarci taron jin bahasi kan garambawul wa kundin tsarin mulki

"Saboda haka, ina farin cikin fada muku cewa kawo yanzu, mun samu ciyar da dalibai kimanin milyan 10, mun dauki masu girki 100,000 aiki," Ta kara.

"Hakazalika muna samar da ayyukan yi da dama irinsu sufuri, aikin noma, da kwanukan zuba abinci."

A riwayar Vanguard, Hajiya Sadiya ta ce shirin ciyar da dalibai na cikin kokarin da gwamnatin Buhari keyi wajen fitar da yan Najeriya milyan 100 daga cikin talauci cikin shekaru 10.

A bangare guda, gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i, yace jihohi ne ya kamata su yanke kwatankwacin yawan kananan hukumomin da zasu iya ɗauka.

Gwamnan yace Najeriya ƙasa ce dake ɗauke da gwamnatocin jihohi 36 da kuma gwamnatin tarayya.

A cewar gwamnan, a lissafo jerin kananan hukumomin ƙasar nan 774 sannan ace ana son maƙala wa gwamnatin tarayya su kai tsaye, wannan ya saɓa wa tsarin mulkin da muke tafiya a kanshi na jamhuriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel