Yanzu-yanzu: An saki Daliban Jami'ar Greenfield dake jihar Kaduna

Yanzu-yanzu: An saki Daliban Jami'ar Greenfield dake jihar Kaduna

- A ranar 20 ga Afrilu, yan bindiga suka kai hari jami'ar Greenfield

- Jami'ar ta kasance makaranta mai zaman kanta a hanyar Abuja zuwa Kaduna

- Bayan sama da wata guda, daliban sun samu yanci

Labarin dake shigo mana da duminsa na nuna cewa yan bindiga masu garkuwa da mutane sun sake daliban jami'ar Greenfield bayan sama da wata guda a hannunsu.

A riwayar Channels TV, dalibai 14 aka sake ranar Asabar.

Shugaban kungiyar iyayen daliban, Markus Zarmai da wasu sun je tarban tarban inda yan bindigan sukayi alkawarin ajiyesu.

Legit ta tuntubi Kakakin hukumar yan sandan jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, kuma ya tabbatar da wannan labari.

A cewarsa, har yanzu yana neman bayani amma lallai akwai magana an saki wasu cikin daliban.

"Akwai wannan maganar cewa an saki wasu cikin daliban," Jalige ya bayyanawa wakilinmu.

Wannan ya biyo bayan maganar Sheikh Ahmad Gumi inda yace yan bindigan sun fasa kashesu kamar yadda sukayi barazana.

DUBA NAN: Dalilin da yasa muka kashe daliban jami'ar Greenfield 5, Masu garkuwa da mutane

Yanzu-yanzu: An saki Daliban Jami'ar Greenfield dake jihar Kaduna
Yanzu-yanzu: An saki Daliban Jami'ar Greenfield dake jihar Kaduna
Asali: Original

KU KARANTA: Mun shawo kan yan bindiga da suka sace daliban Greenfield, ba zasu kashesu ba: Sheikh Gumi

Za ku tuna cewa a ranar 20 ga Afrilu yan bindiga suka kai hari jami'ar dake hanyar Kaduna-Abuja kuma suka hallaka mai gadi.

Sun bukaci kudin fansan N800m, amma da aka ki biyansu bayan kwanki uku, suka kashe dalibai 5 cikin 22 da suka sace.

An tsinci gawawwakin daliban a cikin daji.

A hirar da VOA Hausa tayi da shugaban yan bindigan mai suna Sani Idris Jalingo (Baleri), ya ce sun kashe dalibai biyar ne don nunawa duniya cewa gwamnati ta gaza.

A ranar 3 ga Mayu, yan bindigan sun yi barazanar kashe sauran dalibai 17 dake hannunsu idan gwamnatin Kaduna bata biya kudin fansa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel