Talauci da rashin ilimi ke rura wutan rashin tsaro a Najeriya, Zulum

Talauci da rashin ilimi ke rura wutan rashin tsaro a Najeriya, Zulum

- Gwamnan Zulum ya taya takwaransa na Nasarawa murnar shirin kafa kamfanin sukari a jiharsa

- Zulum ya bashi shawara kan wani mai matukar muhimmanci

- Matsalar tsaro ta zama babban kalubale ga dukkan sassan Najeriya

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya bayyana cewa talauci da rashin ilimi na cikin abubuwan dake rura wutan rashin tsaro a kasar nan.

Zulum ya bayyana hakan ranar Juma'a, a Abuja, a bikin rattafa hannu kan yarjejeniya tsakanin takwararsa gwamnan Nasarawa da kamfanin Flour Mills, rahoton Vanguard.

Gwamnatin Nasarawa ta shiga yarjejeniya da Flour Mills ne wajen kafa kamfanin sukari a karamar hukumar Toto na jihar.

A sakon fatan alheri ga gwamnan Nasarawa, Zulum ya yi kira gareshi ya tabbatar da cewa mafi akasarin ma'aikatan kamfanin yan asalin jihar ne.

Ya ce kafa wannan kamfani zai taimaka wajen samar da aikin yi da kuma habaka tattalin arzikin jihar.

DUBA NAN: Nan da watan Yuli zamu fara ginin layin dogon Kaduna zuwa Kano, Minista Amaechi

Talauci da rashin ilimi ke rura wutan rashin tsaro a Najeriya, Zulum
Talauci da rashin ilimi ke rura wutan rashin tsaro a Najeriya, Zulum Hoto: Governor of Borno
Asali: Facebook

KU DUBA: Ofishoshi 11, motoci 13, da Janareto 429 mukayi asara a hare-hare 41 da aka kai mana, Hukumar INEC

Gwamnan Borno ya ce bakin talauci, rashin ilimi, da rashin adalci, na cikin abubuwa da suka haddasa matsalar tsaro.

"Saboda haka ina baiwa gwamna Sule shawara ya tsara shirye-shirye don tabbatar da cewa an aiwatar da yarjrjrniyar," Zulum yace.

"Ina fatan cewa Kamfanin Flour Mills za ta duba halin da mutan Nasarawa ke ciki, na farko wajen inganta arzikin gida da kuma daukar aiki."

Ya kara da cewa idan Kamfanin tak daukan yan asalin jihar aiki, hakan zai iya haddasa irin matsalar tsaron da ake fuskanta a sauran jihohi a jihar Nasarawa.

A bangare guda, gwamnatin tarayya a ranar Talata ta sanar da cewa ta samu nasarar ciyar da daliban makaranta milyan goma karkashin shirin ciyar da yan makaranta a fadin tarayya watau NHGSFP.

Ministar tallafi, kula da annoba da jin dadin jama'a, Hajya Sadiya Umar Farouq, ta sanar da hakan a Abuja a bikin kaddamar da shirin rabon kayayyakin girki a Abuja, rahoton Punch

A cewar Minista Sadiya, gwamnatin tarayya ta dauki masu girki sama da 100,000 aiki don yiwa daliban abinci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel