Ofishoshi 11, motoci 13, da Janareto 429 mukayi asara a hare-hare 41 da aka kai mana, Hukumar INEC

Ofishoshi 11, motoci 13, da Janareto 429 mukayi asara a hare-hare 41 da aka kai mana, Hukumar INEC

- Shugaban INEC Farfesa Mahmood Yakubu ya yi taron gaggawa kan harkar tsaro a zabe

- Farfesan ya bayyana irin asarar da hukumar tayi cikin shekaru biyu

- Ofishohin INEC na fuskantar barazana musamman a yankin kudu maso gabas

Shugaban hukumar shirya zaben kasa INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu, ya yi gargadin cewa yunkurin kawo hargitsi harkar zabe na iya lalata demokradiyyan Najeriya da kuma rikita kasar.

Yakubu ya bayyana hakan a taron gaggawan da yayi da hukumomin tsaro a Abuja ranar Alhamis kan hare-haren da ake kaiwa ofishohin hukumar musamman a yankin kudu maso gabas, rahoton Punch.

Yakubu yace, "Ko shakka babu hukumar ta shiga wani hali a yan makonnin da suka gabata. Yadda ake babbaka ofishoshin hukumar da lalata dukiyarta babban kalubale ne ga shirye-shiryen zaben da mukayi."

"A shekaru biyu da suka gabata, an samu hare-hare 41 ciki har da wadanda aka kai da gayya. Guda tara a 2019, 21 a 2020."

KU KARANTA: Nan da watan Yuli zamu fara ginin layin dogon Kaduna zuwa Kano, Minista Amaechi

Ofishoshi 11, motoci 13, da Janareto 429 mukayi asara a hare-hare 41 da aka kai mana, Hukumar INEC
Ofishoshi 11, motoci 13, da Janareto 429 mukayi asara a hare-hare 41 da aka kai mana, Hukumar INEC
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kyakkyawar budurwa yar Arewa wacce ta fara tukin jirgi tun tana shekara 17

"A makonni hudu da suka gabata, an kona ofishoshin hukumar 11 kuma an sace kayayyaki. Biyu ciki harin Boko Haram da tsagerun yan bindiga ne yayinda 11 na yan tsageru da yan bangan siyasa ne, " Farfesa Mahmoud ya kara.

"A lokacin zanga-zangan EndSARS a Oktoban bara, an kai hare-hare 18, yayinda wasu yan tsageru suka kai 11."

Mun kawo muku cewa Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) Farfesa Mahmood Yakubu ya yi taron gaggawa kan harkar tsaro a zabe tare da shugabannin hukumomin tsaro a hedikwatar INEC da ke Abuja.

Taron na zuwa ne biyo bayan hare-haren da aka kai kan cibiyoyin INEC a Ebonyi, da wasu wasu jihohin kudu, lamarin da ya jawo jam'iyyar adawa ta PDP ke zargin gwamnati mai ci na shirya makarkashiyar hana zabe a 2023, Vanguard ta ruwaito.

Wadanda suka halarci taron sun hada da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Babagana Mongunu da Darakta-Janar na hukumar leken asiri ta kasa Ahmed Abubakar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel