Mun kwace kayan ado irinsu gwala-gwalai na N14.4bn, gidajen $80m daga Diezani: Hukumar EFCC

Mun kwace kayan ado irinsu gwala-gwalai na N14.4bn, gidajen $80m daga Diezani: Hukumar EFCC

- Majalisar Tarayya ta zargi Ministan shari’a, Abubakar Malami da rashin gaskiya

-Saboda haka an gayyaci shugaban EFCC don bayani

- Hukumar EFCC na karkashin ma'aikatar Shari'a da Malami ke jagoranta

Shugaban hukumar hana almundahanda yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC, Abdulrasheed Bawa, ya bayyana cewa kayan adon da suka kwace daga hannun tsohon ministar mai, Diezani Alison-Madueke ya kai N14.4 billion.

Shugaban EFCC ya bayyana hakan ne ranar Juma'a yayinda ya gurfana gaban kwamitin majalisar wakilai dake bincike kan yadda akayi da kudaden satan da aka kwato, rahoton ChannelsTV.

Yace "kayan adon da aka kwata daga wajen tsohuwar ministar ya kai na kudi N14.4 billion.kamar yadda hukumomin gwamnati suka kiyasta."

Bawa ya kara da cewa kiyasin kudin gidajen da aka kwace daga Diezani ya kai $80 million.

Har yanzu hukumar bata sayar wadannan dukiyoyi ba saboda gwamnati bata bada umurnin haka ba, Bawa yace.

DUBA NAN: Daliban jami'ar Kimiyya ta Wudil sun yi bikin murnar ranar Abaya

Mun kwace kayan ado irinsu gwala-gwalai na N14.4bn, gidajen $80m daga Diezani: Hukumar EFCC
Mun kwace kayan ado irinsu gwala-gwalai na N14.4bn, gidajen $80m daga Diezani: Hukumar EFCC
Asali: UGC

KU KARANTA: Nan da watan Yuli zamu fara ginin layin dogon Kaduna zuwa Kano, Minista Amaechi

Majalisar wakilai ta fara kaddamar da bincike kan dukkan dukiyoyin da hukumomin gwamnati ta kwato tsakanin 2002 da 2020.

A Satumban 2019, babban kotun tarayya dake Legas ta sadaukarwa gwamnatin tarayya kayan adon Diezani Madueke.

Diezani ta kasance Ministar Mai karkashin shugaban Goodluck Jonathan.

A bangare guda, a ranar Talata, 25 ga watan Mayu, 2021, Ministan shari’a, Abubakar Malami, ya bayyana a gaban wani kwamiti na majalisar wakilan tarayya a Najeriya.

Jaridar Premium Times ta ce a karshe, Abubakar Malami ya amsa gayyatar da wannan kwamitin da ke bincike kan kudin satar da aka bankado ta aika masa.

Da ya hallara gaban ‘yan majalisar, Abubakar Malami SAN, ya ce gazawar su wajen amincewa da wani kudiri da aka yi aiki a 2017 ya jawowa gwamnati cikas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel