Daliban jami'ar Kimiyya ta Wudil sun yi bikin murnar ranar Abaya

Daliban jami'ar Kimiyya ta Wudil sun yi bikin murnar ranar Abaya

Dalibai mata a jami'ar Kimiyya da fasaha ta jiha dake garin Wudil, jihar Kano sun yi bikin murnar ranar Abaya a yau Alhamis, 27 ga Mayu, 2021.

Wannan ya biyo bayan sanarwan hukumar jami'ar na ayyana kowace ranar 27 ga Mayu na shekara matsayin ranar bikin Abaya.

Hukumar jami'ar ta yi hakan ne bayan bidiyo ya bayyana wasu dalibai maza suna cin mutuncin wata suna mata isgili don ta sanya Abaya.

Legit ta tattaro cewa Abaya wani tufafi ne da ke rufe jikin diya mace daga sama har kasa kuma an fi sawa bayan kwalliya.

Wannan tufafi ya samu asali ne daga kasashen Larabawa wannan hakan ya bayyana daga kalmar 'Abaya'.

BBC ta ruwaito yadda aka yi bikin inda wasu dalibai mata suka bayyana ra'ayoyinsu kan wannan sabuwar al'ada da hukumar makarantar ta kirkiro.

A cewar rahoton, wasu daliban sun ce yanzu sun fi samun natsuwa wajen saka Abayar.

Kalli hotunan:

Daliban jami'ar Kimiyya ta Wudil sun yi bikin murnar ranar Abaya
Daliban jami'ar Kimiyya ta Wudil sun yi bikin murnar ranar Abaya Hoto: Bappancey/Photography
Asali: Facebook

Daliban jami'ar Kimiyya ta Wudil sun yi bikin murnar ranar Abaya
Daliban jami'ar Kimiyya ta Wudil sun yi bikin murnar ranar Abaya Hoto: Bappancey/Photography
Asali: Facebook

KU KARANTA: Nan da watan Yuli zamu fara ginin layin dogon Kaduna zuwa Kano, Minista Amaechi

Daliban jami'ar Kimiyya ta Wudil sun yi bikin murnar ranar Abaya
Daliban jami'ar Kimiyya ta Wudil sun yi bikin murnar ranar Abaya Hoto: Bappancey/Photography
Asali: Facebook

Daliban jami'ar Kimiyya ta Wudil sun yi bikin murnar ranar Abaya
Daliban jami'ar Kimiyya ta Wudil sun yi bikin murnar ranar Abaya Hoto: Bappancey/Photography
Asali: Facebook

KU KARANTA: Kyakkyawar budurwa yar Arewa wacce ta fara tukin jirgi tun tana shekara 17

Mahukunta a jami'ar kimiyya da fasaha ta Wudil a Jihar Kano ta ce za ta dauki "mummunan mataki" kan daliban da suka cin zarafin wata daliba saboda ta saka rigar abaya.

Cikin wata sanarwa da makarantar ta fitar a jiya Talata ta shafin Tuwita, shugaban sashen harkokin dalibai ya nemi afuwar dalibar sannan ya bukaci ta shigar da kara a hukumance domin neman hakkinta da aka take.

A jiya Talata ne aka ga wasu matasa na jan abaya da wata daliba ta saka tare da yi mata ihu cikin wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta a wani wuri da aka ce cikin jami'ar ne ta Wudil.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng