Sata ta saci sata: Minista ya na taba kudin da aka karbo a wajen barayi inji Majalisar Najeriya

Sata ta saci sata: Minista ya na taba kudin da aka karbo a wajen barayi inji Majalisar Najeriya

- Majalisar Tarayya ta zargi Ministan shari’a, Abubakar Malami da rashin gaskiya

- Ana binciken ofishin AGF, Abubakar Malami SAN da zargin laifin cin kudin sata

- Wani kwamitin Majalisar ya na bincike kan kudin da aka karbo a hannun barayi

A ranar Talata, 25 ga watan Mayu, 2021, Ministan shari’a, Abubakar Malami, ya bayyana a gaban wani kwamiti na majalisar wakilan tarayya a Najeriya.

Jaridar Premium Times ta ce a karshe, Abubakar Malami ya amsa gayyatar da wannan kwamitin da ke bincike kan kudin satar da aka bankado ta aika masa.

Da ya hallara gaban ‘yan majalisar, Abubakar Malami SAN, ya ce gazawar su wajen amincewa da wani kudiri da aka yi aiki a 2017 ya jawowa gwamnati cikas.

KU KARANTA: Ana sauraron zaman Gwamnati da NLC kafin a tsaida farashin mai

Abubakar Malami ya ce kudirin da majalisa ta gagara tabbatarwa ya taimaka wajen samun matsalar tattaro kudin da aka karbe daga hannun barayin kasa.

Ministan ya ce sun yi yunkurin yin gyara; “Ina mai da-na-sanin cewa ba a amince da kudirinmu ba, da an yi wannan, da yanzu wata maganar ake yi dabam.”

Shugaban wannan kwamiti, Honarabul Adejoro Adeogun ya ce akwai hannun Ministan wajen amfani da kudin da aka karbo daga barayi cikin kasafin kasa.

Adejoro Adeogun da ‘yan kwamitinsa suka ce abin da ya kamata shi ne a tattara duk kudin da aka samu zuwa asusun kudin-shiga, ba a kashe kudin kai-tsaye ba.

KU KARANTA: Jagoran Jam’iyya ya na so Magajin Buhari a APC ya fito daga Kudu

Sata ta saci sata: Minista ya na taba kudin da aka karbo a wajen barayi inji Majalisar Najeriya
Abubakar Malami SAN Hoto: @MalamiSAN
Asali: Twitter

Ministan shari’an kasar yake cewa: “Ofishin AGF bai taba karbar sisin kobo daga asusun kudin sata ba, ko da kudin ladar karbo kudin. OAGF ba ya karbar kudi.”

The Nation ta ce Adeogun ya kalubalanci Ministan, ya nuna masa hujja daga CBN da ke nuna kudin da aka karbe daga wajen barayi sun shiga ofishinsa a 2017.

Daga nan Ministan bai iya cewa komai ba, ‘yan majalisar suka nuna ba su gamsu da bayanansa ba.

Dazu kun ji cewa Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III ya nemi sanin nawa aka gano a hannun barayin gwamnati, da kuma abin da ake yi da kudin.

Da yake jawabi wajen wani taro a Sokoto, Muhammad Sa'ad Abubakar ya ce an rubuta littatafan da za su taimaka wajen yaki da barayi a Daular Usmaniyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng