Nan da shekara 2, sai yan Najeriya sun jinjinawa shugaba Buhari: Fadar Shugaban kasa

Nan da shekara 2, sai yan Najeriya sun jinjinawa shugaba Buhari: Fadar Shugaban kasa

- Shugaba Buhari ya cika shekaru shida kan kujerar mulkin Najeriya

- Hadimansa sun lissafa nasarorin da ya samu a wannan shekarun

- Yan Najeriya sun ce rashin tsaro ya karu a cikin wadannan shekaru shidan

Fadar shugaban kasa, a ranar Juma'a, ta bayyana cewa kafin karewar wa'adin shugaba Muhammadu Buhari a 2023, ko masu adawa sai sun jinjinawa masa.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayyana hakan a jawabin murnar cikar Buhari shekaru 6 kan mulki.

Adesina ya lissafa jerin nasarori da ayyukan da shugaba Muhammadu Buhari yayi.

Hadimin ya bayyana cewa gwamnatin maigidansa ta samu dimbin nasarori a bangaren Tattalin arziki, tsaro, samar da aikin yi, jin dadin al'umma, dss.

A cewarsa "wadanda basu bari siyasa ko adawa ya hana su ganin gaskiya ba zasu tabbatar da cewa an yi aiki."

DUBA NAN: An damke hadimin gwamna Sule, yan sanda 2, Kansila da wasu 14 kan satan karafunan layin dogo

Nan da shekara 2, har yan adawa sai sun jinjinawa shugaba Buhari: Fadar Shugaban kasa
Nan da shekara 2, har yan adawa sai sun jinjinawa shugaba Buhari: Fadar Shugaban kasa Hoto: @channelstv
Asali: Twitter

DUBA NAN: Nan da watan Yuli zamu fara ginin layin dogon Kaduna zuwa Kano, Minista Amaechi

Adesina ya ce "Daga ayyukan jin dadi, zuwa harkar kudi, ilimi, wasanni, yaki da rashawa, gine-ginen gidaje, man fetur, harkokin waje, da sauran su, gwamnatin nan ta samu nasarori kuma ya kamata Najeriya suyi alfahari."

"Ga masu cewa: "Ba ma ganin komai da sukeyi. Ba ma samun labarin komai, nan da shekara biyu da ikon Allah, zasu jinjinawa shugaban kasa, har yan adawa mafi tsanani."

A bangare guda, mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar, a ranar Laraba, ya ce yan Najeriya su daina yaudarar kansu cewa abubuwa na tafiya daidai a Najeriya.

Sultan Saad ya bayyana hakan ne a taron tattauna matsalar tsaro dake gudana a Abuja, rahoton Channels.

"Kada mu yaudari kanmu cewa abubuwa na tafiya daidai, abubuwa sun tabarbare. Mun san hakan, kuma muna gani," Sultan yace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel