Da Ɗuminsa: Mutum 10 Sun Mutu Sakamakon Sabon Harin Da Ƴan Bindiga Suka Kai a Kaduna

Da Ɗuminsa: Mutum 10 Sun Mutu Sakamakon Sabon Harin Da Ƴan Bindiga Suka Kai a Kaduna

- Rayyukan mutane 10 sun salwanta sakamakon hari da harin ramuwar gayya a kauyukan Kaduna

- Wasu yan bindiga sun kai hari kauyen Na'ikko a karamar hukumar Giwa inda suka kashe mutum uku

- Daga bisani, matasan Na'ikko sun kai harin ramuwar gayya wata rugar fulani sun kashe mutum biyu

- Yan bindiga sun kuma kai hari kauyen Dakyauro sun halaka mutane hudu sun sace shanu kimanin 25

A kalla mutane 10 ne suka gamu da ajalinsu a hannun yan bindiga yayin hari da harin ramuwar gayya da suka kai a wasu kauyuka da ke karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna a cewar rahoton TVC News.

A cewar kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, yan bindigan sun kai hari kauyen Na'ikko a karamar hukumar Giwa inda suka yi musayar wuta da wasu yan garin hakan ya yi sanadin mutuwar mutane uku yan garin.

Da Ɗuminsa: Mutum 10 Sun Mutu Sakamakon Sabon Harin Da Ƴan Bindiga Suka Kai a Kaduna
Da Ɗuminsa: Mutum 10 Sun Mutu Sakamakon Sabon Harin Da Ƴan Bindiga Suka Kai a Kaduna. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: An Kama Hadimin Gwamna Sule Da Wasu Mutum 16 Kan Satar Kayan Gwamnati

Mr Aruwan ya ce matasan kauyen Na'ikko sun mayar da martani ta hanyar kai hari Rugan Abdulmuminu, wani rugar fulani da ke kusa da su, inda suka kashe mutum biyu da ake zargin sun kai harin farkon.

Yan bindiga sun kuma kai hari kauyen Dakyauro a karamar hukumar Igabi inda suka kashe mutane hudu suka sace shanu kimanin 25. An kuma kashe wani jigo a garin a karamar hukumar Chikun.

Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya nuna bacin ransa game da harin ya kuma mika sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda aka kashe.

KU KARANTA: Sojoji Sun Ragargaji 'Yan IPOB, Sun Kashe 7 Sun Kama Biyar a Rivers

Gwamna El-Rufai ya yi kira ga mutanen kauyen Na'ikko a karamar hukumar Giwa su rika barin doka ta yi aikinta su guji daukan fansa domin hakan ba zai haifar da alheri ba.

Ya bawa manoman kananan hukumomin Igabi, Birnin Gwari, Giwa, Kajuru da Chikun tabbacin cewa gwamnatinsa tana daukan matakan da suka dace domin ganin sun samu damar cigaba da rayuwarsu cikin lumana da zaman lafiya.

A wani labari daban, Ƴan bindiga sun kashe ƴan sa-kai 19 a ƙauyen Yartsakuwa a ƙaramar hukumar Rabah na jihar Sokoto kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wani mazaunin garin, wanda ya yi magana da majiyar Legit.ng a wayar tarho ya ce ƴan sa-kan sun rasa rayukansu ne yayin da suke ƙoƙarin daƙile harin da ƴan bindigan suka kaiwa garin.

Mazaunin garin, da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce yan bindigan sun kai hari ne ƙauyen misalin ƙarfe ɗaya na ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel