Shugaban INEC, EFCC da Sauransu Sun Shiga Dakin Tattaunawar Gaggawa

Shugaban INEC, EFCC da Sauransu Sun Shiga Dakin Tattaunawar Gaggawa

- Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ya shiga taron gaggawa da wasu manyan kasa

- An ruwaito cewa, akwai manyan shugabannin hukumomi da masu fada aji a wajen taron na gaggawa

- Shugaban na INEC ya bayyana shirin hukumarsa ta zaben jihar Anambra da ke zuwa a cikin wannan shekara

Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) Farfesa Mahmood Yakubu ya yi taron gaggawa kan harkar tsaro a zabe tare da shugabannin hukumomin tsaro a hedikwatar INEC da ke Abuja.

Taron na zuwa ne biyo bayan hare-haren da aka kai kan cibiyoyin INEC a Ebonyi, da wasu wasu jihohin kudu, lamarin da ya jawo jam'iyyar adawa ta PDP ke zargin gwamnati mai ci na shirya makarkashiyar hana zabe a 2023, Vanguard ta ruwaito.

Wadanda suka halarci taron sun hada da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Babagana Mongunu da Darakta-Janar na hukumar leken asiri ta kasa Ahmed Abubakar.

KU KARANTA: Sabon Nadi: Sharhin 'Yan Najeriya Game da Nada Manjo-Janar Farouk Yahaya

Shugaban INEC, EFCC da Sauransu Sun Shiga Dakin Tattaunawar Gaggawa
Shugaban INEC, EFCC da Sauransu Sun Shiga Dakin Tattaunawar Gaggawa Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Hakazalika mukaddashin shugaban hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), Abdulrasheed Bawa da mukaddashin Sufeto Janar na ‘yan sanda Alkali Usman sun hallara.

Wadanda suka halarci taron sun hada da wakilan babban hafsan hafsoshin tsaro, da kuma shugabannin rundunonin tsaro, gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Shugaban na INEC ya jaddada dalilin da ya sa aka kira wannan taron gaggawa na tsaro.

Kafin a fara taron, an yi shiru na minti daya don girmama marigayi Babban hafsan sojan kasar Ibrahim Attahiru da kuma wadanda suka mutu tare da shi a lokacin mummunan hadarin da ya afku a ranar Juma’ar da ta gabata a jihar Kaduna.

Shugaban INEC ya bayyana ayyukan da ke gaban Hukumar wanda ya hada da zaben gwamnan jihar Anambra na 6 ga Nuwamba Nuwamba da ci gaba da rijistar masu jefa kuri’a.

KU KARANTA: Zan Bulale Babangida Aliyu: Gwamna Wike Ya Yi Barazanar Zane Tsohon Gwamnan Neja

A wani labarin, Wani rahoto da jaridar Nigerian Tribune ta fitar ya nuna cewa kungiyar Kudancin Kaduna (SOKAPU) da takwararta ta arewa sun amince da raba Kaduna zuwa sabbin jihohi biyu.

Jonathan Asake, shugaban kungiyar SOKAPU ne ya bayyana hakan yayin gabatarwa da kuma kare bukatunsu a kwamitin wucin gadi na majalisar dattijai da kuma majalisar wakilai ta musamman kan sake duba kundin tsarin mulkin 1999 a bangaren shari'a.

Da yake magana yayin gabatarwar, a ranar Laraba, 26 ga watan Mayu, shugaban kungiyar ta SOKAPU ya ce burin kudancin Kaduna shi ne a samar da sabon kundin tsarin mulki, ba wai gyara tsoho ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel