Kyakkyawar budurwa yar Arewa wacce ta fara tukin jirgi tun tana shekara 17

Kyakkyawar budurwa yar Arewa wacce ta fara tukin jirgi tun tana shekara 17

- Wata kyakkyawar yar Arewa, Maira Bashir El-Kanemi, ta zama abin alfahari ga Najeriya

- Wannan budurwa ta fara tukin jirgi tun lokacin da take da shekaru 17

- Bayan shekara guda, ta zama kwararriyar matukiyar jirgi mai lasisi

Maira Bashir El-Kanemi wata kyakkyawar budurwa ce wacce ke da soyayyar tukin jirgi.

Kwanan nan a kafafen ra'ayi da sada zumunta hotunan ta suka bayyana kuma yan Najeriya ke yi mata tofin san barka.

A cewar shafin Arewa Facts Zone dake Tuwita, Maira ta fara tukin jirgi tun tana yar shekara 17.

Maira yar asalin jihar Borno ce kuma yanzu ta samu lasisin tukin jirgi tana yar shekaru 18.

DUBA NAN: Nan da shekara 2, har yan adawa sai sun jinjinawa shugaba Buhari: Fadar Shugaban kasa

Kyakkayawar budurwa yar Arewa wacce ta fara tukin jirgi tun tana shekara 17
Kyakkayawar budurwa yar Arewa wacce ta fara tukin jirgi tun tana shekara 17 Hoto: @OvieAli
Asali: Facebook

KU KARANTA: Nan da watan Yuli zamu fara ginin layin dogon Kaduna zuwa Kano, Minista Amaechi

Kyakkyawar budurwar mai shawa'an zama kyaftan na jiragen kasuwa yanzu haka tana tukin jirgi mai leken asisi da Boeing 737.

@OvieAli ya bayyana bidiyon budurwar a shafinsa tana cikin jirgi.

'Yan Najeriya sun bayyana nasararta a matsayin abin koyi ga sauran yan Najeriya.

Kalli bidiyon:

Asali: Legit.ng

Online view pixel