Shugaban kasar Ghana ya kawo ziyara fadar shugaban kasa, Aso VIlla

Shugaban kasar Ghana ya kawo ziyara fadar shugaban kasa, Aso VIlla

- Shugaban kasar Ghana ya kawo ziyararsa ta farko bayan lashe zaben wa'adi na biyu

- A cikin makon nan, Buhari ya karbi bakuncin shugabannin kasashen Afrika 3

- Na farko shugaban CAR, Sannan na Libya, sai kuma na Ghana

Shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo ya kawo wa shugaba Muhammadu Buhari ziyara fadar Aso Villa a ranar Alhamis, 27 ga watan Mayu, 2021.

Nana Akufo ya dira fadar shugaban kasan ne da rana kuma ya samu kyakkayawan tarba daga shugaba Buhari da kansa da manyan mukarrabansa.

Rahotanni sun nuna cewa Nana ya zo ganawa da Buhari ne kan wasu lamura masu muhimmanci.

KU KARANTA: Nan da watan Yuli zamu fara ginin layin dogon Kaduna zuwa Kano, Minista Amaechi

Shugaban kasar Ghana ya kawo ziyara fadar shugaban kasa, Aso VIlla
Shugaban kasar Ghana ya kawo ziyara fadar shugaban kasa, Aso VIlla
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kyakkyawar budurwa yar Arewa wacce ta fara tukin jirgi tun tana shekara 17

Wannan ya biyo bayan ziyarar da Shugaban kasar Libiya, Mohamed Younis Menfi, ya kaiwa shugaba Buhari a fadar Aso Villa, dake birnin tarayya Abuja ranar Laraba, 26 ga Mayu, 2021.

Menfi ya dira fadar Aso Villa ne misalin karfe 10 na safe kuma Buhari da mukarrabansa suka tarbesa.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa yayi farin cikin karban bakuncin Shugaba Mohammed Younis kuma ya bayyana muhimmancin Libya ga Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel