Shugaban kasar Libya ya kawowa shugaba Buhari ziyara Aso Villa

Shugaban kasar Libya ya kawowa shugaba Buhari ziyara Aso Villa

- Tun bayan mutuwan Gaddafi, an fara tunanin gudanar da zabe a kasar Libya

- Sabon shugaban kwamitin gudanar da kasan ya ziyarci shugaban Buhari

- Buhari ya bayyana amfanin zaman lafiyar Libya ga Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin Shugaban kasar Libiya, Mohamed Younis Menfi, a fadar Aso Villa, dake birnin tarayya Abuja ranar Laraba, 26 ga Mayu, 2021.

Menfi ya dira fadar Aso Villa ne misalin karfe 10 na safe kuma Buhari da mukarrabansa suka tarbesa.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa yayi farin cikin karban bakuncin Shugaba Mohammed Younis kuma ya bayyana muhimmancin Libya ga Najeriya.

"Ina farin cikin tarban shugaban majalisar shugabancin Libya, Mohammed Younis Menfi, a yau. Chadi da Nijar na da iyaka da Libya, kuma makwabtanmu ne, " Buhari yace.

"Duk abinda ya shafesu, ya shafe mu. Zaman lafiya da rashinsa a Libya ya shafemu."

DUBA NAN: Shugaban kasar Mali da Firai Ministansa sun yi murabus

DUBA NAN: Gwamna Bala Muhammad ya halarci taron jin bahasi kan garambawul wa kundin tsarin mulki

Buhari ya kara da cewa ya yi matukar farin ciki shugaban kasar ya ziyarci taron kasashen tafkin Chadi da akayi a Abuja ranar Talata da kansa, domin tattauna abinda ke faruwa a Chadi da tasirin hakan kan tsaron kasashen da makwabtaka.

A bangare shugaban Libya, Mohammed Younis, yace za'a gudanar da zabe nan ba da dadewa ba za'a gudanar da zabe a kasarsa.

Ya kara da cewa akwai kyakkyawar alaka a bangarori daban-daban irinsu man fetur da aikin noma tsakanin Najeriya da Libya kuma hakan na nufin muna bukatan juna.

"Muna kira ga hadin kai, da kuma farfado da hadakarmu ta baya," Menfi yace.

A bangare guda, Gwamatin Najeriya ta fada wa sojojin Mali su yi maza su saki shugaban rikon kwarya na kasar Mali, Bah Ndaw da Firayim Minista, Moctar Ouane.

A wani jawabi da mai magana da yawun bakin ma’aikatar harkokin kasar wajen Najeriya, Ferdinand Nwonye, an soki tsare shugabannin da aka yi.

A ranar Talata, ma'aikatar ta fitar da wannan jawabi a shafin Twitter a madadin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel