Ganduje Ya Yi Barazanar Hukunta Gidjen Mai Marasa Kayan Kashe Gobara

Ganduje Ya Yi Barazanar Hukunta Gidjen Mai Marasa Kayan Kashe Gobara

- Gwamna Dr Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi barazanar hukunta masu gidajen mai da ba su da na'urar kashe gobara

- Gwamnan ya ce gwamnatinsa ba za ta amince da masu gidajen mai da ke saka rayuwa da dukiyar jama'a cikin hatsari ba

- Ganduje ya yi wannan gargadin ne yayin da ya ziyarci wasu mutane da suka kone sakamakon gobarar da ta tashi a gidan mai a Kano a baya-bayan nan

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya umurci gidajen man fetur da ke jiharsa su tanadi kayayaykin kashe gobara ko kuma su fuskanci hukunci, The Punch ta ruwaito.

Wannan umurnin na dauke ne cikn wata sanarwa da Ameen Yassar, Shugaban sashin watsa labarai da hulda da jama'a na gidan gwamnati ya fitar a ranar Talata a Kano.

Ganduje Ya Yi Barazanar Hukunta Gidjen Mai Marasa Kayan Kashe Gobara
Ganduje Ya Yi Barazanar Hukunta Gidjen Mai Marasa Kayan Kashe Gobara. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An Kama 'Likitan' Bogi Da Ke Shiga Daji Yana Yi Wa Ƴan Bindiga Aiki a Katsina

Ganduje ya bada wannan umurnin ne a lokacin da ya ziyarci Asibitin Kwararru na Murtala Mohammed da ke Kano domin duba wadanda gobarar tanka da yi wa rauni a baya bayan nan.

Idan za a iya tunawa a kalla mutane 68 suka kone sakamakon gobara da ta tashi a gidan mai na Al-Ihsan da ke Sharada a Kano.

Wata tanka na juye man fetur ne a ranar Asabar sai gobarar ta tashi.

Gwamnan ya umurci hukumar kashe gobara na jihar ta hukunta masu gidajen wadanda ba su da na'urorin kashe gobara wadanda ke aiki.

KU KARANTA: EFCC Ta Kama Hamshaƙin Ɗan Siyasa Kuma Ɗan Kasuwa a Neja

Ya kuma umurci hukumar ta gargadi masu gidajen mai wadanda na'urorinsu na kashe gobarar ke da matsala yana mai cewa gwamnatinsa ba za ta amince a rika sayarwa mutane fetur a yanayi mai hatsari ba.

"Ya kamata hukumar kashe gobarar ta mayar da hankali wurin bibiyar gidajen mai domin tabbatar suna bin dokoki don tabbatar da tsare rayuka da dukiyoyin mutane," ya kara da cewa.

A wani labari daban, Ƴan bindiga sun kashe ƴan sa-kai 19 a ƙauyen Yartsakuwa a ƙaramar hukumar Rabah na jihar Sokoto kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wani mazaunin garin, wanda ya yi magana da majiyar Legit.ng a wayar tarho ya ce ƴan sa-kan sun rasa rayukansu ne yayin da suke ƙoƙarin daƙile harin da ƴan bindigan suka kaiwa garin.

Mazaunin garin, da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce yan bindigan sun kai hari ne ƙauyen misalin ƙarfe ɗaya na ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel