An Kama 'Likitan' Bogi Da Ke Shiga Daji Yana Yi Wa Ƴan Bindiga Aiki a Katsina

An Kama 'Likitan' Bogi Da Ke Shiga Daji Yana Yi Wa Ƴan Bindiga Aiki a Katsina

- Yan sanda a jihar Katsina sun kama wani ma'aikacin lafiya na bogi da ke yi wa yan bindiga aiki

- Ana zargin Musa Shamsudin, dan shekara 25, da shiga cikin daji yana yi wa yan bindiga da suka jikata magani ya fito

- Yayin da aka kama shi, an same shi da wasu magunguna kuma a halin yanzu ana cigaba da zurfafa bincike a kan lamarin

An kama wani ma'aikacin lafiya na bogi, Musa Shamsudin, a yankin Kankara, wanda ake zargin ya kware wurin yi wa yan bindiga da suka samu rauni magani, Rahoton Vanguard.

An gano cewa wanda ake zargin, Shamsudin, dan shekara 25, dan asalin jihar Kogi ne amma yana zaune a Kankara kuma ya saba shiga daji ya fito domin yi wa yan bindiga aiki.

An Kama 'Likitan' Bogi Da Ke Shiga Daji Yana Yi Wa Yan Bindiga Aiki a Katsina
An Kama 'Likitan' Bogi Da Ke Shiga Daji Yana Yi Wa Yan Bindiga Aiki a Katsina. Hoto: @Channelstv
Asali: UGC

KU KARANTA: EFCC Ta Kama Hamshaƙin Ɗan Siyasa Kuma Ɗan Kasuwa a Neja

Mai magana da yawun yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatarwa manema labarai hakan a ranar Talata.

SP Isah ya ce wanda ake zargin ya bace bayan sace daliban Kankara 300 da yan bindiga suka yi a jihar duk da cewa daga baya an ceto yaran.

Ya ce, "Wani likitan bogi, Musa Shamsudin, 'Mai shekara 25), dan asalin jihar Kogi amma mazaunin Kankara da ake zargin yana shiga daji domin yi wa yan bindiga da suka samu rauni magani yana fitowa.

KU KARANTA: 'Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 10, Sun Wasu Sace Da Dama a Zamfara

"A yayin bincike, an gano wasu magunguna a tare da shi. Ana zargin ya bace daga Kankara a ranar da aka sace yaran makarantar Kankara sannan daga baya ya dawo. Ana cigaba da bincike," in ji SP Isah.

Kakakin yan sandan ya cigaba da cewa yan sandan sun yi musayar wuta da wasu yan bindigan inda a kalla aka kashe biyar sannan aka kama wasu 15.

A wani labari daban, Ƴan bindiga sun kashe ƴan sa-kai 19 a ƙauyen Yartsakuwa a ƙaramar hukumar Rabah na jihar Sokoto kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wani mazaunin garin, wanda ya yi magana da majiyar Legit.ng a wayar tarho ya ce ƴan sa-kan sun rasa rayukansu ne yayin da suke ƙoƙarin daƙile harin da ƴan bindigan suka kaiwa garin.

Mazaunin garin, da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce yan bindigan sun kai hari ne ƙauyen misalin ƙarfe ɗaya na ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel