EFCC Ta Kama Hamshaƙin Ɗan Siyasa Kuma Ɗan Kasuwa a Neja

EFCC Ta Kama Hamshaƙin Ɗan Siyasa Kuma Ɗan Kasuwa a Neja

- Hukumar EFCC ta kama wani hamshakin dan siyasa kuma dan kasuwar jihar Neja, Mohammed Umar bisa zargin damfara

- Hukumar tana Zargin Umar ne da damfarar wani matashi N200,000 da sunan zai nema masa aiki karkashin hukumar kwastam

- Bayan lamushe kudin sai ya gabatar masa da wata takardar bogi da sunan aikin ya samu sannan yana neman cikon N550,000

Hukumar EFCC ta kama wani hamshakin dan siyasa kuma dan kasuwa dake jihar Neja, Mohammed Umar bisa zargin damfarar wani matashi N200,000 wadanda ya amsa da sunan zai nema masa aiki.

Tun farko dan siyasar ya bukaci N750,000 ne don nema masa aiki cikin gaggawa a karkashin hukumar kwastam kamar yadda Vangaurd ta ruwaito.

EFCC Ta Kama Hamshaƙin Ɗan Siyasa Kuma Ɗan Kasuwa a Neja
EFCC Ta Kama Hamshaƙin Ɗan Siyasa Kuma Ɗan Kasuwa a Neja. Hoto: @Vangaurdngrnews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan Sanda Sun Kama Ahmad Isah, Mai Gabatar Da Shirin 'Brekete Family'

Saidai mai neman aiki ya fara bashi N200,000 ne a matsayin somin-tabi, kuma ya yi alkawarin cika masa kudin matsawar ya bayyana masa takardar samun aiki karkashin hukumar kwastam.

Duk da dai alamu sun nuna cewa Umar ya hada kai da wani mutum ne wanda EFCC ta gano sunanshi Alhaji Isa Musa, inda suka gabatar wa mai neman aikin wata takardar bogi a matsayin takardar samun aiki.

A wata takarda wacce jami’in hulda da jama’ar hukumar EFCC ya gabatar, Wilson Uwujaren, ya ce anyi gaggawar kama wanda ake zargin bisa zargin damfara a ranar 18 ga watan Mayun 2021, bayan mai neman aikin ya shigar da kara.

KU KARANTA: An Sallami Malaman Makarantun Frimare 20 Daga Aiki a Niger

“Da farko Umar ya nemi N750,000 daga hannun mai neman aikin don gaggauta samun aikin. Sai dai ya biya N200,000 kuma ya yi alkawarin cika kudin da zarar ya gabatar masa da takardar samun aikin.

“An baiwa matashin takardar saidai ya gano cewa ta bogi ce. Sakamakon hakan ne yasa yayi gaggawar sanar da hukumar EFCC don a nema masa hakkinsa.

“Za a gabatar da wanda ake zargin zuwa kotu don yanke hukunci,” kamar yadda takardar tazo.

A wani labarin rahoton daban, gwamnan jihar Rivers, Nyesome Wike ya zargi tsohon gwamnan jihar Niger, Babangida Aliyu da zaman ɗan leƙen asiri da matsala ga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP.

Da ya ke magana a gidan gwamnati a Port Harcourt a ranar Litinin, Wike ya ce Aliyu mutum ne da ya daɗe yana yaudarar jam'iyyarsu ta PDP ya kuma yi mata zagon ƙasa an 2015, The Nation ta ruwaito. Wike Ya Ce Aliyu 'Ɗan Leƙen Asiri' Ne Kuma Alaƙaƙai Ne Ga PDP.

Gwamnan ya yi wannan jawabin ne yayin martani kan wata hira da aka yi da Aliyu a jaridun ƙasa idan ya zargi Wike da ƙoƙarin mayar da kansa uban jam'iyya kuma kai mulkin kama karya a PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel