'Yan Bindiga Sun Kashe 'Yan-Sakai 19 a Ƙauyen Jihar Sokoto

'Yan Bindiga Sun Kashe 'Yan-Sakai 19 a Ƙauyen Jihar Sokoto

- Yan bindiga da suka kai hari ƙauyen Yartsakuwa sun kashe Jami'an tsaro na Ƴan Sa-Kai 19

- Hakan ya faru ne sakamakon yunkurin dakile harin da yan sa-kan suka yi niyyar yi

- Kansilar Ghandi, Aminu Ghandi ya tabbatar da afkuwar wannan mummunan lamarin

Ƴan bindiga sun kashe ƴan sa-kai 19 a ƙauyen Yartsakuwa a ƙaramar hukumar Rabah na jihar Sokoto kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wani mazaunin garin, wanda ya yi magana da majiyar Legit.ng a wayar tarho ya ce ƴan sa-kan sun rasa rayukansu ne yayin da suke ƙoƙarin daƙile harin da ƴan bindigan suka kaiwa garin.

'Yan Bindiga Sun Kashe 'Yan-Sakai 19 a Ƙauyen Jihar Sokoto
'Yan Bindiga Sun Kashe 'Yan-Sakai 19 a Ƙauyen Jihar Sokoto. Hoto: @Vanguardngrnews
Asali: UGC

DUBA WANNAN: 'Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 10, Sun Wasu Sace Da Dama a Zamfara

Mazaunin garin, da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce yan bindigan sun kai hari ne ƙauyen misalin ƙarfe ɗaya na ranar Lahadi.

"Sun zo ne da nufin kashe ɗaya daga cikin shugabannin ƴan sa-kan a yankin," in ji shi.

An ruwaito cewa ƴan bindigan sun halaka shugaban ƴan sa-kan (da aka ɓoye sunansa) a gonarsa.

Kansilar Ghandi A, Aminu Mua'azu Ghandi shima ya tabbatar da afkuwar lamarin lokacin yana mai cewa 14 cikin yan sa-kan ƴan Ghandi ne sauran biyar ɗin kuwa ƴan wasu garuruwa ne da ke karkashin Ghandi.

Ya ce wasu mutum 5 da aka yi wa munanan rauni a harin suna asibiti ana musu magani

Ya kara da cewa yan bindigan sun sace dabbobi da dama da yanzu ba a tantance adadinsu ba.

KU KARANTA: NSCDC Ta Yi Ram Da Wasu Dillalan Miyagun Ƙwayoyi Biyu a Jigawa

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, ASP Sanusi Abubakar, yayin tabbatar da harin ya ce mutum 10 ne kawai suka mutu cikin ƴan sa-kan.

A cewarsa, yan bindigan sun so shiga ƙauyen Yartsakuwa amma aka dakile harin.

Ya ce bayan yan sa-kan, babu wani mahaluki da aka kashe a garin.

Ya shawarci ƴan sa-kan su rika jiran ƴan sanda kafin su tunkari ƴan bindigan.

A wani labarin daban, 'yan sanda a birnin tarayya Abuja sun kama Ahmad Isah, mai rajin kare hakkin bil adama kuma dan jarida, saboda shararawa wata mari da ake zargi da cin zarafin wata yarinya.

Isah, wanda aka fi sani da 'Ordinary President' ya dade yana gabatar da wani shirin rediyo da talabijin mai suna "Brektet Family".

Al'umma sun yi korafi a kansa ne bayan an gan shi cikin wani faifn bidiyo da BBC Africa Eye ta wallafa yana marin wata mata da ake zargin da cinnawa yar dan uwanta wuta a kai kan zarginta da maita.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel