Kiwo a fili ya sabawa addinin Musulunci, Masari ya goyi bayan gwamnonin kudu

Kiwo a fili ya sabawa addinin Musulunci, Masari ya goyi bayan gwamnonin kudu

- Gwamna Masari ya shiga jerin masu goyon bayan hana kiwon fili

- Gwamnonin Kudu 17 sun hadu a Asaba kan domin haramta kiwon dabbobi a fili

- Fadar shugaban kasa ta ce wannan ba zai magance matsalar tsaro ba

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya mara goyon bayansa kan haramta kiwo a fili da gwamnonin kudancin Najeriya suka yi, inda yace yawo da dabbobi ya sabawa koyarwan addinin Musulunci.

Masari ya bayyana haka ga manema labarai a gidan gwamnatin jihar yayinda ake taron murnar cikarsa shekaru shida kan ragamar mulki, rahoton TheNation.

A fahimtar Masari, ya kamata jihohi su samawa masu kiwo fili domin kiwata dabbobinsu sabanin kiwo a titi.

DUBA NAN: Dakarun sojin Najeriya sun damke masu samarwa Boko Haram man fetur a Yobe

Kiwo a fili ya sabawa addinin Musulunci, Masari ya goyi bayan gwamnonin kudu
Kiwo a fili ya sabawa addinin Musulunci, Masari ya goyi bayan gwamnonin kudu
Asali: Facebook

KU KARANTA: Gwamna Bala Muhammad ya halarci taron jin bahasi kan garambawul wa kundin tsarin mulki

Yace: "Abunda ya kamata muyi shine samar da abubuwan da zai hana makiyaya yawo. Ta wani dalili makiyayan Katsina zasu rika yawo?"

"Makiyaya na yawo ne don abu biyu: Ruwa da ciyawa. Idan zamu samar da abubuwan nan biyu, ta wani dalili zasu yi yawo."

"A fahimtarmu wannan ya sabawa addinin Musulunci kuma babu kyau. Wannan na cikin matsalar da muke fama da ita yau. Ba na goyon bayan a cigaba da kiwo a fili."

Game da yiwa Najeriya garambawul kuwa, Masari ya ce jihohi na bukatan dukiya domin aiwatar da abubuwan da gwamnatin tarayya ta gaza aiwatarwa.

A bangare guda, gwamnonin kudancin Najeriya 17 sun caccaki mai magana da yawun shugaban kasa, Mallam Garba Shehu, bisa jawabin da ya saki "sanarwar da gwamnonin sukayi na haramta kiwo a fili a yankinsu ya saba doka."

Shugaban gwamnonin kudu maso yamma, wanda shine gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya zargi Garba Shehu da yunkurin haddasa rikici a Najeriya da kalamansa, rahoton Vanguard.

Akeredolu ya zargi Garba Shehu da "yiwa wasu mutane aiki wanda hakan ya sabawa ra'ayin yan Najeriya masu son zaman lafiya."

Asali: Legit.ng

Online view pixel