Dakarun sojin Najeriya sun damke masu samarwa Boko Haram man fetur a Yobe
- Rundunar Operation Hadin kai ta kai samame maboyar masu samarwa Boko Haram man fetur a jihar Yobe
- Ta damkesu tare da samun jarka 62 dankare da man fetur tare da motocinsu na kaiwa da kawowa a garin Kurkareta
- Rundunar ta kai samamen ne bayan samun bayanan sirri da tayi na wanzuwar zaman mutanen a yankin
Dakarun sojin rundunar Operation Hadin Kai sun kai samame garin Kurkareta na jihar Yobe inda suka cafke masu samarwa Boko Haram kayan aiki.
Kamar yadda Sahara Reporters ta bayyana, daraktan yada labarai na rundunar sojin kasa, Mohammed Yerima, ya bayyana haka a wata takarda da ya fitar a ranar Laraba a Abuja.
Kamar yadda Yerima yace, wasu daga cikin abubuwan da aka samu yayin samamen da ya samu tallafin 'yan sa kan yankin sun hada da jarka 62 dankare da man fetur wadanda aka boye a gidaje da shaguna daban-daban.
KU KARANTA: Buhari ya dage taron majalisar zartarwa, yana makokin Attahiru da sauran jami'an soji
Kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito, ya kara da cewa an samu motocin masu samarwa 'yan ta'addan kayayyaki masu lambar rijista DAL 626 YE (Kano), GBK 413 GR (Benue) da XA 390 SHN (Borno), duk an kwace.
Yerima yace an samu nasarar kai samamen sakamakon bayanan sirri da mazauna yankin suka bada inda suka ce akwai mai samarwa 'yan ta'addan fetur da sauran kayayyakin bukata.
"Dukkan abubuwan da aka samu tare da wadanda ake zargin suna hannun rundunar soji kuma an fara bincike kafin a mika su ga hukumar da ta dace domin hukunci.
“Rundunar sojin kasan Najeriya a shirye take da cigaba da ayyukanta na ganin bayan 'yan ta'adda a yankin."
KU KARANTA: Jaja Wachuku: Jakadan Najeriya na farko da ya fara yaki da babancin launin fata a UN
A wani labari na daban, 'yan sandan jihar Jigawa sun cafke wasu mutum biyar da ake zargi da kaiwa Malam yakubu Ibrahim hari, shugaban jam'iyyar APC na karamar hukumar Dutse.
Kwamishinan 'yan sandan jihar, Usman Gomna, ya tabbatar da kamen ga manema labarai a garin Dutse a ranar Laraba, The Nation ta ruwaito.
Kwamishinan 'yan sandan yayi bayanin cewa wadanda ake zargin sun kutsa sakateriyar jam'iyyar dake karamar hukumar yayin wani taro da aka yi a ranar Litinin inda suka saka karfin tuwo suka dauka shugaban jam'iyyar zuwa wani wuri da ba a sani ba.
Asali: Legit.ng