Gwamna Bala Muhammad ya halarci taron jin bahasi kan garambawul wa kundin tsarin mulki

Gwamna Bala Muhammad ya halarci taron jin bahasi kan garambawul wa kundin tsarin mulki

- Gwamna Bala na Bauchi ya yabawa majalisa bisa kudirin yiwa kundin tsarin mulkin Najeriya gyare-gyare

- Gwamnan ya bayyana irin nakasun dake cikin kundin tsarin mulkin

- Gwamna Bala ya jaddada goyon bayansa kan samar da karin kananan hukumomi a jihar Bauchi

Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad ya halarci taron kwanaki biyu kan jin bahasin al'ummar Najeriya kan garambawul wa kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da majalisar dattawa ta shirya.

Da yake bude taron da ya gudana a dakin taro na masaukin baki na soji dake fadar jihar, Gwamna Bala ya yabawa matakin majalisa ta tara kan garambawul wa kundin.

A jawabin da Lawal Muazu Bauchi mai tallafawa Gwamnan Bala kan kafafen yada labarai na zamani ya saki, gwamnan yace majalisar ta dauki hanyar sauke nauyin dake kanta na sauraren al'umar da Yayan ta ke wakilta ta hanyar damawa da Yan Najeriya cikin gyaran fuska wa wasu dokokin dake kunshe cikin kundin.

KU KARANTA: Gwamna Bala ya gayyaci Jonathan zuwa Bauchi, Sarki ya ba tsohon Shugaban kasa sarauta

Gwamna Bala Muhammad ya halarci taron jin bahasi kan garambawul wa kundin tsarin mulki
Gwamna Bala Muhammad ya halarci taron jin bahasi kan garambawul wa kundin tsarin mulki
Asali: UGC

DUBA NAN: Gwamnan Bauchi Ya amince ya biya ma ɗaliban Sakandiren jihar kuɗin JAMB da NECO

Ya kara da cewa kundin tsarin mulkin ya gamu da nakasu da mamaya tun lokacin juyin mulkin 1966.

Yace kafin juyin mulkin, shugabannin shiyyoyin Najeriya hudu a wancan lokaci na gudanar da shugabanci ta hanyar dogaro da albarkatun Kasar da Najeriya ke da su.

Gwamna Bala sai ya jaddada goyon bayansa na samar da karin kananan hukumomi da jihohi musamman a jihar Bauchi la'akari da girman Kasar ta da kuma yawan al'umar ta.

Gwamnan yace Najeriya za ta bunkasa karkashin sabon fasalin doka da zai ba sarakuna, Yan sandan jihohi da kananan Yancin kansu.

Gwamna Bala Muhammad ya halarci taron jin bahasi kan garambawul wa kundin tsarin mulki
Gwamna Bala Muhammad ya halarci taron jin bahasi kan garambawul wa kundin tsarin mulki
Asali: UGC

Shima a nasa jawabin, jagoran tawagar ta majalisar dattawa Sanata Abubakar Kyari yace shirin zai tattauna kai tsaye da yan Najeriya kana majalisar ta tara za ta yi aikin tabbatar da wanzuwar dokokin.

Saura da suka yi jawabi yayin taron sun hada da shugabannin majalisun jihohin Bauchi, Borno da Yobe wadanda suka marawa shirin baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng