Garba Shehu ya sani cewa shi fa kawai dan aike ne, yayi hattara da kalamansa: Gwamnonin kudu 17
- Gwamnan jihar Ondo ya caccaki mai magana da yawun Buhari, Garba Shehu
- Gwamnan ya yi magana ne a madadin gwamnonin kudancin Najeriya
- Akeredolu ya ce azarbabin Garba Shehu ya fara wuce gona da iri
Gwamnonin kudancin Najeriya 17 sun caccaki mai magana da yawun shugaban kasa, Mallam Garba Shehu, bisa jawabin da ya saki "sanarwar da gwamnonin sukayi na haramta kiwo a fili a yankinsu ya saba doka."
Shugaban gwamnonin kudu maso yamma, wanda shine gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya zargi Garba Shehu da yunkurin haddasa rikici a Najeriya da kalamansa, rahoton Vanguard.
Akeredolu ya zargi Garba Shehu da "yiwa wasu mutane aiki wanda hakan ya sabawa ra'ayin yan Najeriya masu son zaman lafiya."
A jawabin da hadimin gwamnan kan ayyuka na musamman, Dr Doyin Odebowale, ya saki, ya ce "Wajibi ne Garba ya bayyanawa duniya ainihin wadanda yake yiwa aiki, lallai ya bayyana ba shugaban kasa yake wa aiki ba."
KU KARANTA: Babban Limamim jami'ar UNIMAID zai aurar da 'yayansa 10 rana guda
"Garba Shehu ya saki wani jawabi da sunan cewa shugaba Muhammadu Buhari GCFR ne ya sa shi kan rikicin manoma da makiyaya kuma yana ikirarin jawabinsa ne mafita kan lamarin hare-haren makiyaya," Gwamna Akeredolu yace.
"Ba zai yiwu ya cigaba da boyewa karkashin lemar wasu domin haddasa rikici a Najeriya ba. Mun fahimci cewa wasu mutane yake yiwa aiki."
"Ta yaya za'a ce ministan noma, Alhaji Sabo Nanono da dan aike irin Garba Shehu su fi zababbun shugabannin kudancin kasar nan sanin mafita daga cikin matsalarmu . Hakan na bayyana cewa dan aike irinsa bai san iyakansa ba."
A karshe, gwamna Akeredolu yace ko kafa daya na filin kudancin Najeriya Fulani Makiyaya ba zasu samu nasarar kwacewa daga hannunsu ba.
A bangare guda, haɗakar jam'iyyun siyasa CUPP, ta kira yi shugaban ƙasa Buhari da yayi murabus daga kujerarsa saboda ya gaza wajen daƙile matsalar tsaron dake ƙara taɓarɓarewa a Najeriya.
A wani jawabi da shugaban kwamitin yaɗa labarai na CUPP, Chukwudi Ezeobika, ya fitar, yace ya kamata Buhari yayi murabus saboda gazawar gwamnatinsa ta APC.
Asali: Legit.ng