Ka samar da tsaro ko ka amince ka gaza, Kungiyar dattawan Arewa ga Buhari

Ka samar da tsaro ko ka amince ka gaza, Kungiyar dattawan Arewa ga Buhari

- Bayan tsawon lokaci basu yi tsokaci kan lamura ba, dattawan Najeriya sun caccaki Buhari

- Sun daurawa Buhari laifin abubuwan da ake yiwa yan Arewa a kudu

- Gwamnonin Kudu sun haramta kiwon fili a gaba daya

Kungiyar dattawan Arewa (NEF) ta yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari da ya tabbatar da tsaron Najeriya, ya kare rayukan al'umma ko kuma ya amince ya gaza jagorantar kasar nan.

Kungiyar ta ce yan Arewacin Najeriya dake zama a kudu na rayuwar cin dar-dar saboda barazanar da ake musu.

A jawabin da kakakin kungiyar NEF, Hakeem Baba-Ahmed, ya saki, ya ce mafi akasarin yan Najeriya ba sa son yakin kuma suna son Najeriya ta cigaba da zama daya, rahoton Tribune.

"Kungiyar na jaddada cewa ba zata yarda ayi amfani da siyasa wajen cin mutunci da take hakkin yan Najeriya ba," yace.

"Kungiyar na kira ga Shugaba Buhari yayi amfani da karfin da kundin tsarin mulki ta bashi domin kare kasar da jama'arta, ko kuma ya amince ya gaza jagorantar kasar nan cikin wannan hali mai wuya."

"Wajibi ne a daina kaiwa Fulani da yan Arewa hare-hare a Kudancin Najeriya, kuma a hukunta wadanda suka kashesu."

KU KARANTA: Shugaban kasar Mali da Firai Ministansa sun yi murabus

Ka samar da tsaro ko ka amince ka gaza, Kungiyar dattawan Arewa ga Buhari
Ka samar da tsaro ko ka amince ka gaza, Kungiyar dattawan Arewa ga Buhari Hoto: Presidency
Asali: Twitter

KU KARANTA: Gwamna Bala Muhammad ya halarci taron jin bahasi kan garambawul wa kundin tsarin mulki

A bangare guda, fadar shugaban Najeriya ta bayar da dalilan da suka sa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kasa halartar jana’izar marigayi babban hafsan sojan kasar Laftanal-Janar Ibrahim Attahiru a ranar Asabar.

A cewar mai magana da yawun shugaban kasar, Garba Shehu, Shugaba Buhari ya yi nesa da jana’izar ne don kubutar da ’yan Najeriya da basu ji ba basu gani ba daga cutarwar jami’an tsaro da za su yi kokari don ba wa shugaban kasa damar wucewa.

Ya bayyana hakan ne a ranar Talata lokacin da ya bayyana a wani shirin Labarai na ARISE, na Newsnight. Ya lura cewa shugaban bai so a rufe manyan hanyoyi da kuma a dauke hankali daga "yanayin makoki" da ake ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel