Da duminsa: Shugaban kasar Mali da Firai Ministansa sun yi murabus

Da duminsa: Shugaban kasar Mali da Firai Ministansa sun yi murabus

- Bayan damkesu, shugaban kasa da firai minista sun yi murabus

- Wannan ya biyo bayan zuwa tawagar ECOWAS don sulhu

- Kasar Mali ta shiga cikin wani hali kan lamarin shugabanci

Shugaban kasar Mali da Firam Minista sun yi murabus daga kujerunsu bayan tsaresu da Sojoji sukayi ranar Litinin, wani hadimin sabon shugaban na yanzu bayyana.

"Shugaba Bah Ndaw da Firai Ministansa Moctar Oaune sun yi murabus gaban Alkalai," Baba Cissé, mamban kwamitin sulhu da aka tura wanda kuma hadimi ne ga Kanal Assimi Goïta yace.

"Ana cigaba da tattaunawa domin sakesu da kuma kafa sabuwar gwamnati," ya kara.

Wani mamban kwamitin sulhun na daban wanda ya bukaci a sakaye sunansa ya bayyanawa AFP cewa lallai da gaske Bah ya yi murabus.

Wata tawagar gamayyar kasashen yammacin Afrika ECOWAS ta dira inda aka tsare shugaban lasan da Firai Ministansa a barikin Kati, ranar Laraba domin ganin halin da suke ciki.

Kanal Goïta, wanda shine mataimakin shugaban kasa ya tuhumci Bah Ndaw da Oaune da kin damawa da shi wajen wasu sauye-sauye.

KU KARANTA: Garba Shehu ya sani cewa shi fa kawai dan aike ne, yayi hattara da kalamansa: Gwamnonin kudu 17

Da duminsa: Shugaban kasar Mali da Firai Ministansa sun yi murabus
Da duminsa: Shugaban kasar Mali da Firai Ministansa sun yi murabus
Asali: UGC

DUBA NAN: Dakarun sojin Najeriya sun damke masu samarwa Boko Haram man fetur a Yobe

Gwamatin Najeriya ta fada wa sojojin Mali su yi maza su saki shugaban rikon kwarya na kasar Mali, Bah Ndaw da Firayim Minista, Moctar Ouane.

A wani jawabi da mai magana da yawun bakin ma’aikatar harkokin kasar wajen Najeriya, Ferdinand Nwonye, an soki tsare shugabannin da aka yi.

A ranar Talata, ma'aikatar ta fitar da wannan jawabi a shafin Twitter a madadin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel