Fadar Shugaban Kasa Ta Fadi Uzurin Buhari Na Kin Halartar Jana'izar Janar Attahiru

Fadar Shugaban Kasa Ta Fadi Uzurin Buhari Na Kin Halartar Jana'izar Janar Attahiru

- Kusan mako guda bayan da Najeriya ta yi rashin gwarazan jarumanta, an bayyana dalilan da suka hana Buhari zuwa jana'iza

- Mai magana da yawun shugaban kasa ya bayyana cewa, shugaban bai son tara cunkoso wannan yasa ya kauracewa jana'izar

- 'Yan Najeriya sun yi martani kan lamarin, inda suka bayyana ra'ayinsu game da kauracewa jana'izar da Buhari ya yi

Fadar shugaban Najeriya ta bayar da dalilan da suka sa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kasa halartar jana’izar marigayi babban hafsan sojan kasar Laftanal-Janar Ibrahim Attahiru a ranar Asabar.

A cewar mai magana da yawun shugaban kasar, Garba Shehu, Shugaba Buhari ya yi nesa da jana’izar ne don kubutar da ’yan Najeriya da basu ji ba basu gani ba daga cutarwar jami’an tsaro da za su yi kokari don ba wa shugaban kasa damar wucewa.

Ya bayyana hakan ne a ranar Talata lokacin da ya bayyana a wani shirin Labarai na ARISE, na Newsnight. Ya lura cewa shugaban bai so a rufe manyan hanyoyi da kuma a dauke hankali daga "yanayin makoki" da ake ciki.

KU KARANTA: Jerin Sunayen Mutane 90 da Gwamnati Ke Nema Ruwa a Jallo Saboda Saba Dokar Korona

Fadar Shugaban Kasa Ta Fadi Uzurin Buhari Na Kin Halartar Jana'izar Janar Attahiru
Fadar Shugaban Kasa Ta Fadi Uzurin Buhari Na Kin Halartar Jana'izar Janar Attahiru Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

'Yan Najeriya da dama sun nuna damuwa game da dalilan da suka sanya shugaba Buhari ya kasa halartar jana'izar gwarzon sojan da ya mutu yana yiwa kasa hidima.

Bayan da Garba Shehu ya bayyana dalilan da suka sa shugaban bai halarci jana'izar ba, wasu 'yan Najeriya a shafin Tuwita sun yi martani kan batun nasa.

@lucynbin ta ce:

"Babu bukatar bayani don Allah. Mun gode."

rosewater57 ya rubuta:

"'Fadar shugaban kasa' ta dauki kusan sati kafin ta fito da wannan gurgun uzurin."

KU KARANTA: An Gano Yadda Kasar China Ke Dasa Na'urori Kan Musulman Kabilar Uyghur

A wani labarin, Babban hafsan hafsoshin tsaro, Janar Lucky Irabor a ranar Litinin ya umarci sojoji da su daina jin zafi game da mutuwar Shugaban hafsan sojoji, Laftana-Janar Ibrahim Attahiru da wasu jami’ai 10 a wani hatsarin jirgin sama a Kaduna ranar Juma’a.

Da yake jawabi a gidan Attahiru da ke Abuja yayin addu’o’in kwana uku na Fidau, CDS ya bukaci sojojin su ci gaba da kasancewa masu kwarin gwiwa tare da mai da hankali kan matsayinsu na tsarin mulki, Daily Trust ta ruwaito.

“Sako na ga mambobin rundunar sojojin Najeriya shi ne cewa su ci gaba da jajircewa tare da kwazo kan matsayin su na tsarin mulki a wannan lokacin jarrabawa. Bai kamata karsashinsu yayi sanyi ba game da lamarin da ya faru,'' inji Irabor.

Asali: Legit.ng

Online view pixel