Shugaban hafsan sojoji: Kungiyar Ohanaeze ta bayyana wanda take so a ba mukamin

Shugaban hafsan sojoji: Kungiyar Ohanaeze ta bayyana wanda take so a ba mukamin

- Bangaren matasa na Ohanaeze Ndigbo sun bukaci shugaba Buhari da ya ambaci wani dan kabilar Ibo a matsayin shugaban hafsan soji na gaba

- Manjo Janar Ben Ahanotu, shine zabin da kungiyar matasan kudu maso gabas suka fi so

- A cewar kungiyar, Janar Ahanotu shi ne na biyu a kwamandan marigayi babban hafsan sojojin, Laftanar Janar Attahiru

Kungiyar Matasan Ohanaeze Ndigbo (OYC) ta bukaci Shugaba Muhammadu Buhari da ya nada Manjo Janar Ben Ahanotu a matsayin Shugaban hafsan soji na gaba bayan rasuwar Ibrahim Attahiru.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa matasan sun ce nada Ahanotu wanda suka bayyana a matsayin babban jami'in Ibo a cikin Sojojin Najeriya zai taimaka wajen hada kan kasar.

KU KARANTA KUMA: Mijina ya yi mafarkin haɗarin kwana ɗaya kafin afkuwarsa – Matar matukin jirgin sojin da yayi haɗari

Shugaban hafsan sojoji: Kungiyar Ohanaeze ta bayyana wanda take so a ba mukamin
Shugaban hafsan sojoji: Kungiyar Ohanaeze ta bayyana wanda take so a ba mukamin Hoto: @tolanialli
Asali: Twitter

Kungiyar ta ce ta samu labarin cewa Janar Ahanotu, wanda ake zargin ya fito daga jihar Anambara, shi ne na biyu a mukamin kwamanda na marigayi shugaban hafsan sojojin, Laftanar Janar Attahiru.

Legit.ng ta tattaro cewa kungiyar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da shugaban ta, Mazi Okwu Nnabuike da sakatare-janar, Comrade Obinna Achionye suka saki a ranar Talata, 25 ga watan Mayu.

Sanarwar ta yi ikirarin cewa Ahanotu a halin yanzu shi ne Shugaban Manufofi da Tsare-tsare na Sojojin Najeriya.

Ta kara da cewa shi memba ne na kwas na 35 kuma shi ne kwamandan rundunar da ta kame wanda ya kafa kungiyar Boko Haram, Mohammed Yusuf, da mabiyansa.

KU KARANTA KUMA: Bakin ciki da tashin hankali a Benuwe yayin da Makiyaya suka kashe Manoma sama da 100 a garuruwa 4

A gefe guda, hukumar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta hada wani kwamiti da zai binciki hadurran jirgin sama da ke ci gaba da faruwa.

Wannan na zuwa ne a cikin damuwar da ‘yan Najeriya suka nuna biyo bayan hadarin jirgin sama uku da ya faru a cikin watanni uku.

Hadarin ya haifar da asarar rayukan jami'an sojoji 18, ciki har da na makon da ya gabata, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar shugaban hafsan sojin Najeriya, Janar Ibrahim Attahiru, Vanguard News ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel